Spread the love

Uwargidan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fita daga cikin kasar Nijeriya wata biyu da suka wuce yanzu, abin da ya karkato hankalin mutanen fadar shugaban kasa to a ina ta shiga wannan tsawon lokaci ba wani labarinta.

Wasu majiyoyi sun ce ta fita kasar ne domin nuna bacin ranta ga abubuwan da ke faruwa a fadar shugaban kasa.

Uwargidan shugaban kasa ta bar Nijeriya farkon watan Agusta in da ta tafi aikin Hajji tun a wancan lokacin ba ta dawo kasar ba.

Wata majiyar ta ce bayan kammala aikin Hajji ta bar Saudiya ta tafi London, kuma ba a san ranar da za ta dawo ba.

An daina ganinta musamman a wajen taro da kuma lokacin tafiye-tafiyen mijinta wanda ba a saba ganin haka ba.

Duk kokarin da aka yi domin jin ta bakin jami’inta mai kula da harkokin yada labarai Suleiman Haruna ya ci tura domin sanin in da Uwar gidan shugaban kasa take a yanzu.

A baya an sha gani da jin yanda Aisha Buhari ke nuna rashin gamsuwarta ga yanda abubuwa ke tafiya a fadar shugaban kasa da yanda wasu mutane su ka hana gwamnati tafiya yanda yakamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *