Spread the love

Wata Yarinya mai suna Zainab Ibrahim yar shekara 17 da haihuwa tayi karar Mahaifin ta Malam Ibrahim Yunusa Mai Maciji Dadin-Kowa da Dan sa wato Yayan ta Yusuf Ibrahim a gaban kotun yanki ta Bolari a fadar jihar bisa zargin sun yi mata ciki.

A zantawar Zainab da manema labarai kafin a shiga kotu, tace Yayanta Yusuf Ibrahim, shi ya fara kwanciya da ita a lokuta daban daban da ta sanar da Mahifin ta abunda ke faruwa shi ma sai ya nuna bukatar yana son hakan da taki sai ya lallashe ta yana cewa ya za’ayi ta Yarda da Yayanta shi kuma Mahaifinta ta hana shi idan ba ta yarda ba ba za ta yi albarka ba.

Tace shi ne ta yarda ba dan tana so ba har cikin su ya shiga shi ne take neman yadda za’ayi domin cikin yana wata takwas da kwanaki yanzu kuma ba ta jini waye zai dauki nauyin cikin a tsakanin Babanta da kuma Yayan nata.

“Babana ya kwanata dani ba adadi haka shi ma Yayan nawa haka da ciki ya shiga tun yana karami na gaya musu basu ce komai ba shi ne na kai su kara wajen human right su kuma suka sa na kai su kotu” Inji Zainab.

A lokacin da aka shi ga gaban kotu da kotu ta tambayi Zainab ko menene yasa take Karar Mahaifinta da Yayan ta sai tace dukkan su suna kwanciya da ita cikin dare a lokuta mabanbanta, har a wani lokaci da misalin karfe daya Babanta ya shigo dakin ta ya nemeta taki anan ne yake cewa ya za ta yarda da Yayanta shi kuma taki yarda da shi.

Tace tana rokon kotu da ta bi mata kadun ta dan cikin ta ya girma ba ta san waye zai dauki dawainiyar ta ba.

Da kotu ta juywa ga shi Mahaifin na ta yace ya za’ayi yana Mahaifin ta ya kwanta da ita shi bai taba kwanciya da ita ba sai dai a lokacin da ta samu cikin an kawo mata kayan aure dama Mahaifiyar ta da yake basa tare ta turo ta wajen sa ya basu kudi a cikin sadakin da aka bayar na auren ta naira dubu goma dan a zubar da ciki ya nema kuma ya bayar

Yace ya bada kudin ne dan a zubar da cikin kar wanda zai auren ta ya gane ya fasa asirin su ya tonu shi yasa amma shi yasan bai yiwa yarsa ciki ba kuma Yayan nata da take zargi bai san menene a tsakanin su da ita ba.

Lauyan da zai tsayawa Yarinyar mai suna Y.G Ahmed, ya shaidawa kotu cewa karkashin sashi na 211 karamin kashi na ( 2) na kundin tsarin mulki ya nuna cewa laifi irin wannan babbar kotu ce take da hurumin sauraron sa dan a matsayin sa na lauyan gwamnati sun karbi shari’ar za ta koma karkashin ofishin Kwamishinan shari’ar na jiha.

Nan take Alkalin kotun Garba Abubakar Dule, ya gamsu da hakan ya mika karar zuwa ga shi lauyan gwamnati tare da dage karar zuwa ranar 10 ga watan Oktoba na wanann shekarar dan jin yadda karar za ta kasance inda aka salami Uban aka ce ya dawo a wannan ranar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *