Spread the love

Hukumar gudanarwar Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, a jihar Kaduna a Najeriya, ta tabbatar da hukuncin kora da kuma wasu hukunce-hukuncen na daban a kan malamai da ma’aikatanta 15 bisa zargin laifukan da suka hada da neman mata dalibai na jami’ar.

Daraktan sashen hulda da jama’a na jami’ar, Dakta Isma’il Shehu ne ya bayyana wa BBC hakan inda ya ce zarge zargen da ake yi wa ma’aikatan da matakin korar ya shafa sun hada da neman dalibai mata da sakaci da aiki da cin amanar koyarwa har ma da magudin bayar da maki.

Ya ce hukumar jami’ar ta dauki wannan matakin ne sakamakon tsawon lokacin da ta dauka wajen yin nazari da binciken zarge-zargen da nufin tabbatar da gaskiyar tuhume-tuhumen da ake yi wa malaman.

Dakta Shehu ya ce: ”Ma’aikatan sun hada da malamai da wasu da suke aiki a sassa daban daban na jami’ar.”

Da yake tsokaci kan irin hanyoyin da hukumar jami’ar ta bi kafin daukar matakin korar, daraktan ya ce an ziyarci sashen da malaman suke aiki domin tantance laifin da ake zargin sun aikata sannan kuma aka je ga ofishin shugaban jami’ar da kwamitin ladabtarwar jami’ar domin hukunta su, kamar yadda daraktan ya bayyana.

Dakta Shehu ya ce, ”akwai wadanda ba a kai ga matakin hukumar koli ta nuna rashin gamsuwarta da bayanan kare kai da suka gabatar ba inda ya ce sai an tsefe bayanansu kafin su ma a san matakin da ya fi dacewa a dauka a kansu’.

Ya kara da cewa wannan ba shi ne karon farko da jami’ar ta dauki irin wannan mataki ba, ikirarin da ya soke zargin da ke cewa hukumar jami’ar ba ta daukar hukunci mai tsauri kan ma’aikatan jami’ar da ake zargi da irin wadannan laifuka.

A baya ma an zargi wasu malaman jami’o’in da irin wadannan dabi’u da suka yi kamari a manyan makarantun Najeriya.

Ko a shekarar da ta gabata ma, an samu wani malami a jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife a jihar Osun, ta Najeriyar, da kokarin tilasta wa wata dalibarsa yin jima’i da ita domin ya ba ta maki., wanda hakan ya kai ga kora da gurfanar da shi a kotu, har aka yanke ma sa zaman gidan yari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *