Spread the love

‘Yan sanda a jihar Neja sun kama daliban jami’ar Ibrahim Madamasi Babangida dake garin Lapai jihar Neja su Takwas kan zarginsu da yin fashi da makami.

Daliban an zarge su da tayar da hankalin ‘yan uwansu dalibai in da suke tare su a dakunan kwanansu na cikin makaranta suna karbe kudinsu da abubuwan amfani.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar DSP Mohammad Abubakar ya ce wadanda ake zargi an kama su ne bisa ga korafin wadanda suka rika yi wa fashin.

A labarin da muke da shi ‘yan fashi da makamin sun kwashe sati uku suna wahalar da daliban a dakunan kwanansu da gidajen dalibai dake cikin makaranta.

A tabakin DSP Abubakar daya daga cikin wadanda ake zargin Yakubu Isah an gane yana cikin ‘yan fashin  ta hanyar wani da suka taba yi wa fashi a dakinsa a 22 ga Satumbar 2019.

Duk a wannan ranar wata da ake kira Hauwa Ibrahim da wasu mutum biyar sun kawo korafi a ofis na ‘yan sanda cewa wasu bata gari dauke da muggan makamai sun kawo masu samame daki bayan daki sun raunata wasu dalibai sun kwace kudin mutane da ba a san yawansu ba.

Mutanen da ake zargi sun hada da Ahmad Kamaldeen da Mohammad Ahmed Hassan da Victor John Dizawo, Abdurrahaman Solomon Baje, Hassan Suleiman, Yakubu Isah Kopa, David Solomon da Umar Abdulkareem Sani.

DSP ya ce har da tabar wiwi aka samu dakin Yakubu lokacin kamen da zaran an kamala bincike za a kai wadan da ake zargi gaban kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *