Spread the love

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce ya umarci lauyoyinsa su dauki matakin shari’a kan Frank da Katch Ononuju kan zargin bata masa suna da suka yi.

Osinbajo ya ce kwanan nan labarun karya da cin zarafi suna yawo a kafafen yada labarai kansa, kafafen sada zumunta na zamani sun tallabi lamarin da girma kusan ko’ina kana ganinsu.

“Ina sanar da ku na bayar da umarnin a dauki matakin shari’a kan wadan nan mutane biyu Timi Frank da Katch Ononuju da suka sanya kansu cikin wannan karyar da shirme” a cewar Osinbajo.

Ya ce “Zan jingine kariyar da tsarin mulki ya bani na wanke sunana ga abin da wadan nan makaryatan suka fada kaina” in ji shi.

Timi Frank tsohon mataimakin sakataren yada labarai ne na jam’iyar APC a ranar Litinin data gabata ya ce abubuwan da ke faruwa ga Osinbajo ba su da alaka da 2023, sama da fadi ne aka yi da wasu biliyan 90 wadanda ake zargi an karbo daga hukumar tattara kudin shiga ta kasa(FIRS) aka tallafi harkokin zaben 2019 da su.   

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *