Kungiyar Kwadago reshen jihar Kebbi ta yi watsi da maganar gwamnatin jihar Kebbi kan karancin albashi na dubu 30(30,000).

Ciyaman na kungiyar a jihar Alhaji Umar Halidu ne ya sanar da hakan alokacin da yake yi wa manema labarai jawabi a birnin Kebbi, ya ce daukar matakin kin amincewa da maganar gwamnati hukunci ne aka yanke a zaman tattaunawa da mambobin kungiyar na kananan hukumomi 21 na jihar.

“Bayan mun dubi lamarin karin albashin na dubu 30 da ya mamaye kafofin sada zumunta na zamani kungiyar da ta ‘yan kasuwa da TUC mun yi watsi da maganar gwamnati na aminta da fara biyan mafi karancin albashin” Ya ce

Ya cigaba da cewa amincewa ce da ba ta da makama, ya za a ce gwamnati za ta fara biyan mafi karancin albashi ba tare da yin wata yarjejeniya da kungiya ba.

Ya kara da cewa ‘Ba mu san kaso nawa aka karawa ma’aikacin da ya haura matakin albashi na bakwai ba. Mafi karancin albashi na dubu 30 daga bakin mataki na daya zuwa na shida doka ce, wadanda suka haura matakin suna son sanin nasu abu ne da yakamata mu tattauna da gwamnati akai matsaya’ in ji shi.

Ciyaman ya ce rashin sanya kungiya a wurin daukar matakin sabawa tafiyar hadin kai ce, “don haka muka nisanta kanmu ga maganar karin albashi”.

Ya yi kira ga gwamnati ta tsaya ta yi abin da zai zama gamsasshe ga jama’a. Ma’aikata kuma su zama masu biyar doka da oda su zauna lafiya a tsakaninsu. “Kungiya za ta yi komai don kwato masu hakkinsu da kare martabarsu”. Ya ce

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *