Spread the love

Dan majalisar Wakillan Nijeriya ya yi kira ga ma’aikatar lafiya ta gwamnatin tarayya da fitar da tsarin yakar ciwon zazzabin cizon sauro ko maleriya ga mutanen kasa a dukan asibitocin gwamnati.

Haka kuma ya yi kira cibiyar hana yaduwar ciruta da su dauki matakin hana yaduwar annobar Lassa a jihar Benue kar abari ta yadu cikin kasa.

Wannan ya biyo bayan aminta da wasu kudurori biyu “Na sake duba tsarin kawar da Maleriya a Nijeriya” Wanda Benjamin Bem Mzondu da “Duba Annobar Lassa” da Robert Aondona Tyough suka gabatar.

Benjamin ya ce kashi 76 na al’ummar Nijeriya cutar Maleriya mai tsanani ta shafe su, kashi 24 ne ke dauke da karancin ciwon.

A wurin bayar da gudunmuwa a zauren majalisa Chris Ngoro ya ce an gano a kowace shekara mutum dubu 300 ke mutuwa kan Maleriya duk ana kashe biliyan 132 ga yin maganinta.

Bayan miliyan 900 na sayen maganin maleriya a kowace shekara ake samun wannan rasa rayukkan wadanda mafi yawansu mata ne da kananan yara. A kwai bukatar canja salon yakar cutar a Nijeriya. a cewar Managarciya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *