Spread the love

MATSALAR HANYA DAGA KOKO ZUWA YAURI A JIHAR KEBBI.

Ƙaramar hukumar Koko zuwa Yauri Wannan shi ne wuri mafi muni kan hanya wanda ke cikin garin Saminaka karamar hukumar Mulki ta Shanga .

Yanzu haka an samu cinkuson na manyan motoci saboda rashin kyawon hanyar wanda akalla akwai manyan motoci (tanki da tirela)sama ga mota ashirin suna jiran masu aikin taimakon sakai matasa daga kauyunkan dake kusa ga hanyar wadanda suke tsaye suna taimakawa domin babu wurin wucew gashi ana cikin lokacin damana ne

Yanzu haka wannan yasa motoci na nan na yunkurin fasa daji musamman kananan motoci domin samun wurin wucewa

Ita dai wananan hanya ta taso daga jihar Sokoto tabiyo cikin jihar kebbi har zuwa jihar Neja wadda tun 2012 aka fara aikin ta amma dab da tsakkiyar wannan shekarar ta 2019 sai kamfanin dake aikin hanyar ya dakatar da aikin har zuwa yanzu babu wani labari na dawowar kamfanin domin cigaba da aikin kuma wannan yanki yana cikin mazabar kebbi ta kudu karkashin
Sanata Bala Ibni na Allah.

Tsawon shekarru gwamnatin tarayya ta bayar da aikin gyaran hanyar daga Sokoto zuwa Kontagora amma har yanzu ba a kammala aikin ba fiye da shekara shida.

Daga
Sani Musa Saminaka
Shanga kebbi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *