Spread the love

Rikici ya mamaye jam’iyar APC in da shugabannin jam’iyar na jihohi 36 dana birnin tarayya suka yi metin na gaggawa a Abuja don yin tir da yanda harkokin jam’iyar ke gudana.

Sun koka yanda jagororin APC suka kasa riƙe nasarorin da jam’iyar ta samu sun fita batunta nasarar tana rawa.

A takardar bayan taro na shugabannin jam’iyar suka fitar ta nuna rashin gamsuwarsu ga yanda jam’iyar ke tafiya an jefar da kowane ɓangaren jam’iya.

Takardar wadda shugaban jam’iyun da sakatarensu Ali Bukar Bolari da Ben Nwoye suka sanyawa hannu ciyamomin jam’iyar ne a jihar Borno da Enugu.

A cikin ƙorafe ƙorafensu an jefar da su ga yin muƙaman gwamnatin tarayya.

Abu mafi muni a jam’iyar an ƙyale shugabanni suna tafiyar da jagoranci ba sakatare na ƙasa.

Sun baiwa jam’iyar kwana 10 daga sanda labari ya fita su ɗauki matakin gyaran jam’iyar tun daga matakin mazaɓa, ƙananan hukomomi da jihohi gaba ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *