Spread the love

Wakili a majalisar tarayyar Nijeriya Ahmadu Jah dake wakiltar kananan hukumomin Dambow da Gwaza da Chibok (APC Borno) ya ce masu tayar da kayar bai sun mamaye kananan hukumomi 8 cikin 10 na Arewacin jihar borno.

Jaha ya fadi haka ne a zauren majalisa a lokacin zaman majalisa da yake bayar da ta shi gudunmuwa kan bukatar saka kudi na musamman ga harkar tsaron Nijeriya.

Dan majalisan ya zargi yaki da rashin tsaro a kasar nan ana boye-boye kansa.

“Dauki misali a karamar hukumata ta Gwaza dake da Mazaba 13 mazaba uku ko hudu ne kawai Boko Haram ba su mamaye ba.”

“A Chibok akwai mazaba 10 mazaba biyu kacal ce Boko Haram ba su mamaye ba. A Dambuwa muna da mazaba 10 daya ce kawai ba su mamaye ba. Wannan kawai fa kananan hukumomin da nake wakilta ne” a cewarsa..

Ya ce bulaliyar majalisa Sheda ne a cikin kananan hukumomi 10 biyu ne kadai hidikwatarssu ‘yan boko haram ba su mamaye ba.

Mai magana da yawun sojoji Kanal Sagir Musa ya ki magana a lokacin da aka tuntube shi.

Ya ce ba shi ne yakamata ya yi magana ba .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *