Spread the love

Hukumar kula da sadarwar zamani ta Nijeriya ta fara binciken manhajar Turukola(truecaller) kan tonon asirin da take yi wa ‘yan Nijeriya.

A bayanin da hukumar ta fitar wanda babban Darakta Kashifu Abdullahi Inuwa ya sanyawa hannu ya ce manhajar ts sanya ɗimbin ƴan ƙasa cikin rashin tabbas.

Inuwa ya ce sun samu cikakken bayani manhajar ta saɓawa dokokin duniya dana Nijeriya na amfani da sadarwa musamman.

Ya ce wasu tanade-tanaden manhajar tsari ne ƙarara na cin zarafin masu amfani da ita. Wannan shiri ne da bai dace ba don ya sa da yawan mutanen ƙasa ba su da sirri.

Ya ce da yawan mutane ba su san ba abin da suke sanya manhajar na buɗe nambar da aka rufe lokacin kiransu kawai take yi ba.

In kana son kasan abubuwan da suke yi ka dubi tsarin amfani da manhajar a rubutunsu na huɗu za ka samu.

Akwai buƙatar ‘yan Nijeriya su goge wannan manhajar gaba ɗaya daga cikin wayoyinsu.

Hukumar za ta tabbatar da ta kare haƙƙin ‘yan ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *