Spread the love


Daga Alaji Ibrahim Ismail.
 Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, a jiya Litinin ya kaddamar wani shafin yanar gizo wanda zai tattara bayanan mutane milyan 2 daga dukkan kananan hukumomin jihar 27 domin samar musu da aikin yi.
 Dakta Babagana Mustapha shi ne Kwamishinan Sabuwar Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha da ker-kere ta jihar Borno, kuma shi ke da alhakin kula da shafin, ya bayyana cewa manufar bude shafin shi ne a samar da wata rumbun yanar gizo da zata tattara bayanan dukkan masu neman aiki a jihar, wanda za’a samar musu aiki a mataki na kasa da jiha da kuma Karamar hukuma, hakazalika za’a iya anfani da bayyanan wurin samar musu aiki a ma’akatun da bana Gwamnati ba.
Gwamna Zulum ya ba da umarni ga Ma’aikatar Kimiyya da Fasahar da ta hada kai da ma’aikar ilimin sadarwa da kuma sashin yada labarai na gidan gwamnati wajen samar da cibiyar yanar da a dukkkan kananan hukumomi 27.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *