Abin da ‘yan kwankwasiya suka yi wa shaikh Pantami ba su kyauta ba

Daga Datti Assalafiy.

Wasu daga cikin gamayyyar ‘yan jam’iyyar Kwankwasiyya sun yiwa Maigirma Ministan Sadarwa Dr Isah Ali Ibrahim Pantami mummunan rashin mutunci da cin zafari yau Talata a filin tashi da saukar jiragen sama dake birnin Kano.

Maigirma Ministan sadarwa Dr Isah Ali Ibrahim Pantami yana kan hanyarsa ne daga Katsina ya dawo Kano zai wuce Abuja ta jirgi, su kuma marassa mutuncin ‘yan darikar Kwankwasiyya sun raka abokansu filin jirgi zasu tafi wata kasa wai karatu, shine suka hadu da tawagar Minista suka masa mummunan cin zarafi da rashin mutunci.

A daidai lokacin da wannan mummunan al’amari ya faru ina tare da makusantan Malam muka yanie shawaran kada mu fitar da abin har sai idan su ‘yan Kwankwasiyyar ne suka fara fitarwa, to da yake mutanen banza ne basu da mutunci sai suka fitar don su tabbatarwa duniya cewa su marassa mutunci ne tsageru masu fada da Malamai Magada Annabawan Allah.

Laifin me Dr Isah Ali Ibrahim Pantami ya muku da ku kai masa haka, ko da ba don kasancewarsa Minista ba amma ai Malamin addinin Musulunci ne, Mahaddacin Qur’ani da Hadisi, ba zaku duba wannan darajar da Allah Ya masa ku kiyaye martaba da mutuncinsa ba?

Hoto na uku da na saka a wannan rubutun Minista ne Dr Isah Pantami da wacce ta tsaguna ta haifi Sarkinku, ina nufin mahaifiyarsa maimartaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi, ku duba kuga yadda Malam ya nuna ladabi da biyayya ga mahaifiyar Sarkin da kuke marukar kauna an dauki hoton shekaran jiya lahadi a birnin Kano kafin ya wuce garin Katsina.

Na rantsa da girman Allah ban taba jin tarihin mutanen da sukayi fada da Malamai sukaci nasara ba, wallahi wannan abinda kukayi madugunku kuka ciwa mutunci, Allah ne kadai ya san miliyoyin mutane da zasu kulla kiyayya da darikar kwankwasiyya sakamakon wannan mummunan laifi da cin zarafi da kuka aikata wa babban Malamin addinin Musulunci na duniya.

Har a gurin Allah Dr Isah Ali Pantami yafi Kwankwaso daraja, domin Mahaddacin Qur’ani ne da Hadisi, Malamin addinin Musulunci ne da yake shiryar da bayin Allah zuwa ga tafarkin tsira, a ilmin addini da na boko yafi Kwankwaso Plumber nesa ba kusa, to ina yafi madugunku daraja.

Mun bawa Kwankwaso lokaci kankani, wallahi tallahi ya fito ya bada hakuri sannan ya nesanta kansa da wannan mummunan al’amari da wawayen mabiyansa suka aikata, idan kuma yaji dadin hakan muna rokon Allah Ya haramtawa Kwankwasiyyah mulki har abada, Allah Ka shafe tasirin siyasarsu a duniya Amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *