Spread the love

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya cika alkawarin da ya dauka  ya sanya danshi Abubakar Sadiq a makarantar Gwamnati.

Managarciya ta ruwaito Gwamnan a safiyar yau ya sanya yaronsa ne a Capital School

Abin jira a gani ko akwai abin da zai sauya ga makarantar da sauran makarantun gwamnatin jihar Kaduna.

‘Yan siyasa a Nijeriya an sansu da sanya siyasa a kowane lamarin rayuwa da suke yi to wannan lamarin da Gwamna ya yi za a zuba ma shi ido a gani shin yay i haka ne domin inganta makarantun gwamnati a jiharsa ko kuma domin ya janyo hankalin mutane ga kansa domin cimma burinsa da ake  ganin ya sa a gaba a 2023.

Ko mine ne anan dai yay i kokari ya zama gwamna na farko a wannan wa’adi da sanya dansa makarantar gwamnati da fatar wasu Gwamnoni za su yi koyi da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *