Spread the love

A ranar Lahadi ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kama hanyarsa zuwa birnin New York da ke Amurka domin halartar taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 74.

Ana ganin cewa wannan taron da shugaban kasar zai halarta na da matukar muhimmanci ga Najeriyar ganin cewa an zabi dan Najeriya wato Tijjani Muhammad Bande a matsayin Shugaban Babban Zauren Majalisar.

A kwanakin baya ne dai aka zabi Farfesa Tijjani Muhammad Bande a matsayin shugaban.
Maudu’in da za a tattauna a zauren shi ne ” Fargar da kasashe wajen yaki da talauci da samar da ingantaccen ilimi da kuma daukar matakai kan sauyin yanayi.”

Za a fara tafka muhawara a zauren ne a ranar Talata 24 ga watan Satumba a inda shugabanni za su yi jawabai game da kasashensu, kazalika za su yi bayanai kan maudu’in taron na wannan shekara.

Ana sa ran Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari shi ne mai magana na biyar a wurin taron.

Wannan ne karo na biyu da Najeriya ke samun gurbin shugabanci a Babban Zauren Majalisar Duniya, inda a shekarar 1989, Manjo Janar Joseph Garba ya zama shugaba.

Ana sa ran Shugaba Buhari zai mayar da hankali ne wajen bayani kan ci gaban da ya samu musamman ta bangaren alkawuran da ya yi a lokacin yakin neman zaben 2015 da kuma 2019.

Wadanda suka hada da samar da tsaro da yaki da cin hanci da rashawa da kuma habaka tattalin arziki.

Sai dai a wata sanarwa da babbar jam’iyyar hamayya ta kasar wato PDP ta fitar ta bayyana cewa shugaban ba shi da wani abin kirki da zai bayyana ko kuma ya yi tinkaho da shi a wajen taron.

Sanarwar da jam’iyyar ta fitar ta hannun mai magana da yawunta Kola Ologbondiyan ta bayyana cewa zai halarci taron ne ba tare da wasu manufofi ko tsare-tsare ba da za su kawo ci gaba ga Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *