Spread the love

Gwamnatin jahar Zamfara ta yi nasarar karbo mutum 30 a hannun masu garkuwa da mutane, mutanen wadanda aka sako sun hada mata 15 maza 15.

Daga cikin matan da aka sako hudu daga cikinsu Suna shayarwa ne, Wanda daya daga cikinsu da aka karbo ta haihu ne, a hannun masu garkuwa da mutanen.

Mutanen da da aka karbo, an karbo su ne, a dajin Maradun, kuma mafiya yawansu sun kwashe sama da watanni biyar-biyar hannun masu garkuwar yayinda wasu su ka kwashe sama da watanni takwas.

Sako wadannan mutanen zuwa yanzu dai an sako Sama da mutum Dari uku tun bayan da wannan Gwamnatin ta Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun ta hau kan karagar mulki watanni Kasa da hudu da su ka gabata. Kuma duk wannan ta faru ne, sanadiyar shirin sulhu da Gwamnatin ta yi da su masu garkuwa da mutane din. Wanda tuni Gwamnatin ta dauki hanyoyin inganta rayuwar da su al’ummar da su ka dauki makamai, Wanda zuwa yanzu da dama daga cikinsu Mika makamansu ga ita wannan Gwamnatin.

Da ya ke Jawabi bayan karbo wadannan mutanen Mai baiwa gwamnan Zamfara Shawara na musamman a bangaren tsaro Hon. Abubakar Justice Dauran ya bayyana cewa: “Wadannan mutanen mun karbo su ne a cikin dazukkan Maradun, kuma Gwamnatin jahar Zamfara za ta kula da lafiyar wadannan mutane kamar yadda ku ka ganmu a Assibiti, sai duk sun dawo cikin hayacinsu daga nan sai mu hannunta ta ga iyalansu.

Domin akwai wadanda ba ma ba ‘yan asalin jahar Zamfara ba. Wanda insha allahu zaman lafiya ya samu a jahar Zamfara.

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *