Kungiyar mabiya addinin kirista reshen jihar Kaduna ta bayyana rashin jin dadinta dangane da yunkurin gwamnati na rusa cocin Anglican na Saint Geoges da ke Sabon garin Zaria, wanda aka gina tun a shekarar 1908.

Reverend Hayab, shine Shugaban Kungiyar ya Kara da cewa mafi Yawan wadanda suke Mulki a yanzu ba a haife su ba lokacin da aka gina cocin”.

Hayab ya karyata cewa an bai wa cocin diyya inda ya ce Muna zaune kawai sai muka ga wasika wai za a rushe coci saboda an biya kudin diyya, alhali Ba bu wanda ya biya diyya”

“Na biyu wasikar kuma ba ta da kwanan wata a jikinta. Shi ya sa muke neman gwamnatin jihar ta Kaduna ta fada mana tana da masaniya kan wannan wasika idan ba haka ba kuma muna son ta hukunta duk mai hannu a al’amarin.”

Majiyar mu ta BBC dai ta yi kokarin tuntubar Kwamishinan harkokin cikin gida na jihar Kaduna, wanda shi ne mai magana da yawun gwamna, Mr Aruwan domin jin nasu bangaren, amma ba a yi nasara ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *