Spread the love

Mataimakin shugaban kasar Nijeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ce wasu mutane ne yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zagon kasa.

Ya ce Buhari ya gadi dimnbin matsaloli da mataccen tattalin arziki ga gwamantin da ta gabata ta Jonathan, Buhari na daukar matakan da suka dace don samar da jin dadi ga ‘yan Nijeriya.

Mataimakin shugaban kasa ya yi wadan nan kalamai ne a wurin bukin binne mahaifiyar sakataren hukumar yaki da cin hanci da rashawa Ola Olukoyode a cocin Ikere a jihar Ekiti.

Da yake yi wa mahalarta taron jawabi ya ce ƙasar Nijeriya tana buƙatar kowa ya sa hannunsa a yi aiki tuƙuru, ‘ni ɗan jam’iyar APC nejam’iyar Awolowo, ba gaskiya ba ne a ce Shugaba Buhariya bai san yanda ake shugabanci ba. Ba haka ba ne domin ya yi iyakar ƙoƙarinsa. Masu zagon ƙasa ne ta ko’ina suna yaƙarmu amma dai ba za su yi nasara ba. Abin da Buhari ya ƙudurta na ciyar da ƙasar nan gaba sai ya cika shi.

“Abubuwan cigaban jama’a da walwala irinsu Tireda Moni da N-power nan gaba kaɗan za a ga amfaninsu” a cewarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *