Spread the love

Kalaman zargin karbewa mataimakin Shugaban kasa karfin iko da jagoranci suna kara yawaita a cikin al’ummar  Nijeriya.

Kalaman sun fara bayan fitar da sabbin sunayen mutanen da za su rika baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tattalin arzikin kasa, in da suka maye kwamitn da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ke jagoranta.

Ba tare da fadada jawabi ba mai Magana da yawun shugaban kasa Femi Adeshina ya ce sabon kwamitin kai tsaye za su yi hulda da shugaban kasa game da abin da ya shafi aikin da aka damka masu.

Kafin kare maganganu kan canja kwamitin na Osinbajo sai ga maganar datse karfin ikonsa na duba wasu hukumomin gwamnati da yake yi a takardar bayanan da aka tura masa.

Osinbajo ne shugaban  gudanarwa na hukumar kula da agajin gaggawa(NEMA) da hukumar cigaban mutanen kan iyakoki(BCDA) da (NIPSS) da hukumar iyakoki(NBC).

Haka kuma shi ne jagoran daraktocin hukumar bayar wutar lantarki ta Neja Delta(NDPHC)  da kwamitin sayar da kadarorin gwamnati.

Majiyoyi har da fadar shugaban kasa sun bayyana wannan abin da aka yi ma shi bai da alaka da 2023 a lokacin da Buhari zai kamala wa’adinsa na biyu kenan.

Wata majiyar ta ce maye gurbin kwamitin Osinbajo da aka yi ba wai don kwamitin bai yi kokari ba ne sai dai kan maganar siyasar 2023 ne.

“Dole ‘yan Nijeriya su rika tofa albarkacin bakinsu su dubi kilan wannan abin da aka yi wani bangare ne na fadan da ake yi tsakanin Nasir El-Rufa’I da Tinubu da Osinbajo kansa.”

“Ba za ka kore wadan nan jita-jitar ba domin hakan na cikin siyasa da gwamnati. Akwai bukatar shugaban kasa ya yi Magana kan lamarin don shi zai sa wutar ta mutu a yanzu.” A cewar Majiyar

Rashin bayar da wasu hujjoji da ‘yan kasa za su ji su gamsu kan abin da aka yi wa mataimakin shugaban kasa, zai sa a cigaba da yada jita-jita har a fito da wani abu da baikamata ba.   

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *