Spread the love

TSARAWA DA GABATARWA Bashir Abdullahi El-bash.

-Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Ya Buɗe Wani Sabon Katafaren Masallacin Juma’a Da Islamiyya Wanda Gidauniyarsa Ta Gina A Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa.

-An Yabawa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje Kan Ƙoƙarinsa Na Yaƙi Da Cutar Foliyo Fiye Da Kowane Gwamna A Shiyar Arewa Maso Yammacin Nageriya.

-Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Ya Halarci Bikin Buɗe Wani Katafaren Gidan Mai Mafi Girma A Jihar Kano.

Yau Juma’a, 20 ga watan Satumba, 2019.
Kamar yadda aka saba, (Jihar Kano A Mako Mai Ƙarewa, shiri ne na musamman da ke yin duba kan wasu muhimman batutuwan da su ka faru a Jihar Kano da ma wajen Jihar, waɗanda su ke da alaƙa da gwamnatin mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda ni Bashir Abdullahi El-bash na ke rubutawa na tsara na kuma gabatar muku a duk ranar Juma’ar ƙarshen mako.

A cikin shirin na yau, za ku ji cewa:

(1). A wannan mako mai ƙarewa ne, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta, Abdullahi Umar Ganduje, ya aika saƙon taya murna ga mai girma shugaban ƙasa, Mallam Muhammadu Buhari dangane da samun nasara da ya yi a kotun sauraren ƙararrakin zaɓe cikin wata ƙara da jam’iyyar PDP da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Alhaji, Atiku Abubakar, su ka shigar gabanta kan ƙalubalantar nasarar da shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC su ka samu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2019.

Cikin kalmomin da ya furta, gwamna Ganduje ya bayyana cewa “wannan hukunci da kotun ta zartar, shi ya ƙara tabbatar da cewa dukkan tsare-tsare da hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan zaɓe sahihai ne ingantattu, an yi zaɓe na gaskiya”.

Sannan kuma, mai girma gwamna ya ƙarƙare da fatan cigaba da samun nasara ga mai girma shugaban ƙasa, Mallam Muhammadu Buhari, kamar yadda ya ce:

“Mai girma shugaban ƙasa, hakan na nuni da ka cigaba da aiwatar da kyawawan ayyukan alkhairan da ka faro a zangon mulkinka na farko, akwai ƙarin alkhairai da dama da za su cigaba da wanzuwa a wannan gwamnati ta jam’iyyar APC”. Inji Gwamna Ganduje.

(2). A yunƙurinsa na kaucewa bayanin da ke cewa, “ilimi ba tare da kykkyawan tsarin abinci ba, musamman ga makarantun kwana, sunansa rusasshe”, a wannan mako mai ƙarewa ne, gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya sabunta tsarin ciyar da ɗalibai da ke karatu a makarantun kwana na sakandire.

A kwai makarantun kwana a ƙalla guda (70) a ƙarƙashin wannan tsari, waɗanda su ke da yawan ɗalibai a ƙalla guda (100,000) da za su amfana. Daga cikin jimillar waɗannan makarantu, guda (12) na kimiyya ne da fasaha, (Science And Technical Schools). Wasu (12) kuma makarantun allo ne, (tsangaya schools). Guda (46) kuma, su na ƙarƙashin ma’aikar kulawa da manyan makarantun sakandire, wato (Kano State Senior Secondary School Management Board).

Ya yin da ya ke gabatar da jawabi, gwamnan Ganduje ya bayyana cewa: “hanyace mai tsawo wajen tabbatar da nasarar sabon tsarin da mu ka bijiro da shi na fara bayar da ilimi kyauta tun daga firamare har zuwa babbar sakandire, tare da tsari na musamman ga makarantun kwana na sakandire”.

Mai girma gwamna, ya kuma yi ƙarin haske da cewa, “ya zama wajibi dukkan waɗanda mu ka ba wa wannan kwangila su fahimci cewa a yanzu Jiharmu ta na kan wani sabon tsari ne na ilimi”.

Domin kaucewa dukkan wata matsala da ka iya tasowa ta haifar da cikas kan sabon tsarin ba da ilimi kyauta kuma wajibi a Jihar Kano, musamman ga makarantun kwana, mai girma gwamna ya samar da tsari na musamman wanda ƴan kwangilar za su bi domin ƙoƙarin tabbatar da cewa an inganta harkar ciyar da ɗaliban. Tayadda za a samu nasarar haifar da ɗa mai ido.

“Akwai hanyoyi a ƙalla guda uku waɗanda ya zama wajibi ku bi domin ganin ɗalibanmu sun samu nutsuwa a ya yin ɗaukwar darasi. Hanya ta farko, ku tabbatar kun ba su wadataccen abinci. Hanya ta biyu, ku tabbatar kun ba su abinci mai inganci. Hanya ta uku, ku tabbatar kun ba su abincin akan lokaci”. Inji Gwamna Ganduje.

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a ya yin wani taro da ya gudana a tsakaninsa da mutanen da ya ba wa kwangilar ciyar da ɗaliban da ke karatu a makarantun sakandire na kwana a ɗakin taro mai suna (Africa House), wanda ke cikin gidan gwamnatin Jihar Kano.

(3). Bayan shafe tsawon watanni (6) su na aikin bincike da nazari kan wuri da kuma abubuwan buƙata domin tsugunnar da fulani makiyaya wuri guda, gami kuma da samar da kasuwar sayar da nono, a wannan mako mai ƙarewa ne, kwamitin ya miƙa rahoton binciken da ya gudanar ga mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, a zauren majalissar zartarwa ta jiha da ke fadar gwamnatin Jihar Kano.

Kwamitin mai ɗauke da mutane (26), ƙarƙashin jagorancin Dakta Jibirilla Muhammad, ya ƙunshi masana da ƙwararru a fannoni daban-daban, kama daga kan jami’an tsaro, da likitocin dabbobi, da fulani makiyaya, da malaman makaranta da sauransu.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya kafa kwamitin a ranar 18 ga watan Ogusta, 2019, domin su gudanar da bincike kan wuri da kuma abubuwan buƙata wajen samar da rugar zamani ga fulani makiyaya a Jihar Kano.

Da ya ke gabatar da jawabi a ya yin miƙa rahoton ga mai girma gwamna, shugaban kwamitin, Dakta Jibilla Muhammad, ya bayyana cewa: “mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Jihar Kano a ƙarƙashin jagorancinka, ita ce Jiha ta farko wacce ta fara rungumar wannan aniya da ta haifar da ruɗani ta samar da rugar zamani ga fulani makiyaya a duk Nageriya.

Sannan kuma ya ƙara da yabawa mai girma gwamna kan yadda ya tunkari wannan ƙuduri gadan-gadan, kamar yadda ya ce: “mai girma gwamna, a ya yin da sauran takwarorinka su ka nuna ƙyama kan kan wannan aniya ta zamanantar da tsarin kiwon dabbobi, kai kuwa sai ka kalli ƙudurin a matsayin wani al’amari da zai taimaki cigaban tattalin arziƙi, sannan ka yi watsi da duk wata farfaganda da aka yi ta yaɗawa kan ƙyamatar wannan aiki, kafa wannan kwamiti da ka yi, shi ya ƙara bayyana himmatuwarka kan wannan aiki”.

Shugaban kwamitin, ya kuma ƙara da gabatar da bayani cewa, kafin su cimma matsayar da su ka ɗauka, sun ziyarci dazuka har guda (5) da ke sassa daban-daban na Jihar Kano. Daga cikin dazukan da su ka ziyarta, sun haɗa da:

Dajin Dansoshiya, wanda ke ƙaramar hukumar Ƙiru, da dajin Fanyabo, wanda ke ƙaramar hukumar Doguwa, da dajin Duddurum Gaya, wanda ke ƙaramar hukumar Ajingi, da Dajin Dunawa, wanda ke ƙaramar hukumar Maƙoda, sai kuma wasu yankuna na ƙaramar hukumar Bichi.

Kuma daga ƙarshe sun cimma matsaya kan zaɓar dajin Dansoshiya a matsayin inda za a tsugunnar da fulani makiyaya. Kamar yadda ya ce:

“Biyo bayan dogon nazari cikin nutsuwa da tattaunawa gami da bin diddigi da aunawa, gami da duba da manufofi da burukan da gwamnati ta ke da su kan wannan aiki, kwamitinmu ya zaɓi dajin Dansoshiya na ƙaramar hukumar ƙiru, a matsayin wurin da gwamnati za ta ƙaddamar da wannan aiki”.

(4). A Wannan mako mai ƙarewa ne, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje tare da sauran takwarorinsa gwamnoni, da shugaban jam’iyyar (APC) na ƙasa, Comrade, Adams Oshimole, su ka ziyarci mai girma shugaban ƙasa, Mallam Muhammadu Buhari a fadarsa ta shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja, su ka taya shi murnar samun nasarar da ya yi a kotun sauraren ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa.

(5). A wannan mako mai ƙarewa ne, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya halarci sallar jana’izar marigayi Alhaji Abba Shayi Dambatta, a garin Dambatta, wanda ya ke mahaifi ne ga babban sakataren hukumar kyautata walwala da jindaɗin alhazai ta Jihar Kano, wato Mallam Muhammad Abba Ɗambatta.

(6). A wannan mako mai ƙarewa ne, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya halarci wani taro na musamman wanda ƙungiyar manoma ta ƙasa (AFAN) ta shirya masa shi da sabon ministan aikin gona na ƙasa, Alhaji Sabo Nanono kan taya su murnar cika kwanaki ɗari a kan gadon mulki.

(7). A wannan mako mai ƙarewa ne, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya karɓi baƙuncin babban kwamanda rundunar sojin sama, IA. Amadu, tare da ƴan tawagarsa na ƙasa da kuma babban kwamandan rundunar na Jihar Kano, waɗanda su ka kawo ziyarar aiki Jihar Kano daga hedikwatar rundunar sojin sama da ke Abuja.

(8). A wannan mako mai ƙarewa ne, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ziyarci dajin Falgore inda jami’an tsaro su ka kama ɓarayin shanu da masu garkuwa da mutane. Kuma a cikin jawabin da ya gabatar, gwamna Ganduje ya ba da tabbacin gwamnatinsa kan cigaba da tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Jihar Kano.

(9). A wannan mako mai ƙarewa ne, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya karɓi baƙuncin tawagar (Tax Appeal Tribunal) na shiyar Arewa maso Yamma a ƙarƙashin jagorancin shugabansu, Barista Umar M. Adamu. Inda su ka ziyarci Jihar Kano, domin gudanar da taronsu na masu ruwa da tsaki.

(10). A wannan mako mai ƙarewa ne, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya halarci bikin buɗe wani sabon katafaren gidan mai mafi girma a Nageriya, wanda fitaccen ɗan kasuwar nan ɗan asalin Jihar Kano, mamallakin gidajen man nan mai suna (SALBAS OIL AND GAS), Alhaji Saleh Baba Rano, ya samar da shi a daidai gadar Tamburawa kan titin zuwa Zariya A Jihar Kano.

(11). A wannan mako mai ƙarewa ne, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya halarci taron ƙungiyar gwamnoni na ƙasa (NGF), wanda shugaban ƙungiyar gwamnonin, gwamnan Jihar Ekiti, Mista Fayemi ya jagoranta a sakatariyar ƙungiyar da ke Abuja, babban birnin tarayyar Nageriya.

(12). A wannan mako mai ƙarewa ne, cibiyar da ke nazari kan cutar Foliyo a ƙasa gaba ɗaya, ta aike da sakon yabo da lambar girmamawa ga mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta, Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin gwamnan da ya fi kowane gwamna yaƙi da cutar Foliyo a shiyar Arewa maso Yammacin tarayyar Nageriya.

(13). A wannan mako mai ƙarewa ne, uwar gidan gwamnan Jihar Kano, Hajiya Dakta Hafsat Umar Ganduje (Gwaggon Kanawa) ta samu matsayin (Associate Professor) wanda majalissar zartaswa ta Jami’ar tunawa da Maryam Abacha, wato (Maryam Abacha American University) ta ba ta.

(14). A wannan juma’a ta ƙarshen wannan mako, ina tsaka da haɗa wannan shiri ne kuma, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya buɗe wani katafaren masallacin Juma’a haɗe da makarantar Islamiyya wanda gidauniyarsa, wato (Ganduje Foundation) ta gina a garin Dambazau Gangaren Dutse, a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa.

Daga cikin muhimman mutanen da su ka halarci bikin buɗe masallaci da Islamiyyar, sun haɗa da: Mai girma mataimakin gwamna, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, da mai martaba sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero, da Shaik Abdullahi Pakistan, da Shaik Ƙaribullah Mallam Nasiru Kabara, da Shaik Sidi Musal Ƙasuwuni, da shaik Bashir Usman Zangon Barebari, da Mallam Sani Abdullahi Tofa.

(15). A wannan rana, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya jagoranci tawagar gwamnatinsa inda su ka je Unguwar Sharaɗa su ka yi wa zaɓaɓɓen ɗan majalissar wakilai mai wakiltar birnin Kano a zauren majalissar wakilai na tarayya, Mallam Sha’aban Ibrahim Sharaɗa ta’aziyyar rasuwar mahaifinsa Mallam Ibrahim Sharaɗa, wanda Allah ya karɓi rayuwarsa a jiya, Alhamis, bayan wata gajeruwar rashin lafiya da ya yi.

A ya yin ziyarar ta’aziyyar, mai girma gwamna ya samu rakiyar mataimakinsa, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, da kuma tsohon mataimakin gwamnan Jihar Borno, Alhaji Jatau, da shugaban jam’iyyar (APC) na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas Sunusi, (Ɗan Sarki), da shugaban ma’aikata na gidan gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Ali Haruna Makoɗa, sai kuma shugaban ma’aikata, Mallam Kabiru Shehu, tare kuma da tsaffin kwamishinoni da tsaffin masu ba wa gwamna shawara da mataimaka na musamman da sauran masoya da masu fatan alkhairi.

(16). A wannan mako mai ƙarewa ne, gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya jagoranci tawagar gwamnatinsa inda su ka halarci bikin rantsar da sabon (Grand Khadi) Mallam Tijjani Yusuf Yakasai.

A ya yin zuwa wurin bikin, mai girma gwamna ya samu rakiyar mataimakinsa, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, da kuma tsohon mataimakin gwamnan Jihar Borno, Alhaji Jatau, da shugaban jam’iyyar (APC) na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas Sunusi, (Ɗan Sarki), da shugaban ma’aikata na gidan gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Ali Haruna Makoɗa, sai kuma shugaban ma’aikata, Mallam Kabiru Shehu, tare kuma da tsaffin kwamishinoni da tsaffin masu ba wa gwamna shawara da mataimaka na musamman da sauran masoya da masu fatan alkhairi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *