Spread the love

Matan gwamnonin Arewa sun haɗu don gudanar da zaman tattaunawa na kwana biyu daga ranar 17-18-2019 na Satumba a garin Minna jihar Neja, a ƙarƙashin jagorancin shugabar ƙungiyar Matan gwamnonin Arewa Dakta Amina Abubakar Bello.

Taron ya fara da gaisuwa ta musamman ga Gwamnan jihar wato Alhaji Abubakar Sani Bello ya yi masu fatan Alheri acikin shirye shiryensu da suka sa gaba.

Matan gwamnonin sun gabatar da zama daga bisani sun bude kafar yaƙi da shaye-shaye wanda gwamnan jihar Neja ya jagoranta tare da matan gwamnonin 15 na Arewa. An gina gidan shekara talatin da suka wuce amma ya daina amfani kafin yanzu.

Sun kuma sake shirin akan yaƙi da fyaɗe ga ƙananan yara mata da cutar da yara wanda zasu ƙaddamar chikin watani masu zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *