Spread the love

Daga Rilwanu Labashu Yayari.

Kotun zaben gwamna a jihar Neja ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da dan takararta Umar Nasko suka shigar kan Gwamna Abubakar Bello na jam’iyyar APC.

Jam’iyyar PDP da dan takararta suna kalubalantar nasarar Bello a zaben gwamna da aka gudanar kwanan nan, cewa gwamnan ya gabatar wa da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da takardun shaidar karatu na bogi.

Kotun zaben karkashin jagorancin John Igboji, yayinda yake watsi da karar yace yana cike da tozarta tsarin kotu saboda wata babbar kotun tarayya ta riga ta saurari karar sannan ta yanke hukunci.

Haka zalika kotun zaben ta riki rashin amincewar wacce ake kara na biyu (APC) akan karar da Umar Nasko da PDP suka shigar kan zargin takardun bogi akan Gwamna Abubakar Bello, kan dalili iri guda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *