Mutum 13 ne suka rasu a wani hadarin mota da ya faru kusan Unguwar Ciyawa a karamar hukumar Eggon a jihar Nasarwa.

Kwamanadan kiyaye hadurra na jihar Isma’ila Kugu ne ya sanar da Manema labarai, wadanda suka samu hadarin manyan mutane 10 ne kananan yara uku

Ya ce akwai wasu mutum 11 da suka samu raunuka a hadarin.

Ya kara da cewar Sun janye gawarwakin da wandanda suka samu rauni, sun kai su babbar asibitin Eggon.

Yace hadarin ya faru ne tsakanin babbar mota da bus wadda take mallakar kamfanin zirga-zirga na jihar Benue da wata bakar mota.

Shedun gani da ido ya ce Bus da babbar mota ne suka zoji junansu suka kasa rike motoncin sai mai bakar motar ya sha su ya fadi gefen hanya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *