Spread the love

A cikin mace mai juna biyu dubu 100, dubu da 75 ke mutuwa a Sokoto saboda karancin kayan gina jiki.

Daraktan Kula da cirutoci da rigakafi a hukumar kula da lafiya matakin farko Dakta Hadiza Bodinga ta fitar da bayanin a wajen kaddamar da shirin hukumar USAID da ACTION NIGERIA mai suna ‘Albishirinku’.

Shirin an fitar da shi ne da nufin magance mace-macen kananan yara da masu juna biyu.

Ta bayyana karancin ilmi da kudin shiga ga mata yana haifar musu da tabarbarewar lafiyarsu a lokacin da suke da juna biyu.

Ta ce a cikin yawan mutane 5.3 Miliyan a Sokoto masu dauke da juna biyu za su kai dubu 265, da 667.

A ceawarta kashi 24.3 ke zuwa asibiti yin Awon ciki sauran suna haihuwa a gidajensu saboda karancin ilmin da suke da shi.

Ta kara da cewar cikin masu zuwan kuma kashi 21 ne kadai ke sake zuwa asibiti bayan sun haihu a bincike lafiyarsu.

Akwai bukatar canja wannan halin a wannan jihar domin ba abu ne mai kyau ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *