Spread the love

Lauyoyin dan takarar shugaban kasa na jam’iyar PDP Alhaji Atiku Abubakar sun dogara da hujjoji guda uku da za su sanya kotun koli ta kasa ta hambarar da gwamnatin Buhari in da za ta yi watsi da nasarar da ya samu a kotun sauraren karar shugaban kasa a Laraba da ta gabata.

Atiku da jam’iyarsa za su kalubalanci hukuncin alkalan kotun Tarabunal suka zartar na tabbatar da nasarar da shugaba Buhari ya samu a zaben shugaban kasa da aka yi a 23 Fabarairun 2019.

Atiku ya tafi Tarabunal kan ta soke nasarar da Buhari ya samu a zangon wa’adin mulkinsa na biyu, Kotu ta yi watsi da zarge-zargensa kan kasa gabatar da hujjoji kwarara da za su gamsar da kutun, a jawabin da jagoran alkalan ya karanta na awa Takwas.

Hujja ta farko da za su kalubalanci Buhari da ita, magana kan takardun makarantarsa.

Hujja ta biyu maganar na’urar tantance kuri’u da ke kira Server

Hujja ta uku Maganar soke kuri’u. Don baya yiwuwa a zaben majalisar tarayya a rumfar zabe a ce ba a yi na shugaban kasa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *