Spread the love

Gwamnatin jahar sakwato karkashin jagorancin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, tana iya bakin kokarinta na ganin cewa mata da kananan yara sun samu ingantaccen kiwon lafiya, ta hanyar samarda abubuwan da suke inganta tsarin kiwon lafiya a kowane mataki a fadin jahar sakkwato. Wannan ya hada da samarda kwararrun ma’aikata, magunguna, da shiraruwan wayar da kan alumar da dai sauransu.

uwar gidan gwamnan Sokoto Hajiya Mariya Aminu Waziri Tambuwal ta sanar da hakan a wurin bukin ƙaddamar da shirin ‘Albishirin ku’ wanda aka gudanar a ɗakin taro na makarantar hardar ƙur’ani ta sarkin Musulmi Macciɗo.

Ta ce “Har ila yau gwamnatin jahar sokoto na iya bakin kokarinta na ganin cewa an rage yawan mace macen mata masu juna biyu da kananan yara. Abunda ya dade yana damun wannan gwamnatin. Akan hakane gwamnatin ke maraba da shiraruwa da kungiyoyi domin bada tallafi a wannan haujin musamman kungiyar amurka wato USAID.”

“Zanyi amfani da wannan dama domin gabatarda wannan shirin na Albishirin ku! a jahar sakkwato, shirin daya kunshi hanyoyi da dama domin wayarda kan alumma da ilmantardar dasu matakan daya dace su dauka akan inganta lafiyar mata da kananan yara, samarda abinci mai gina jiki da kuma kariya daga zazzabin cizon sauro wato (malaria). Ina kira ga jama’ar jihar Sakkwato dasu karbi wannan shiri da hannu bibbiyu domin alkhairi ne.”

“A wannan lokaci ina mika godiyata ga kwamitin tuntuba da ilmantarda alumma wato Social and Behavior Change Advocacy Core Group (SBC- ACG) bisa kokarin da sukeyi don ganin an samarda ingantaccen kiwon lafiya da kuma wayarda kan alumma da sukeyi akan abubuwan da suka shafi kiwon lafiya a jahar Sakkwato.”

“Daga karshe inason in mika godiyata ga kungiyar Breakthrough Action Nigeria na ofishin USAID bisa ga shirye shiryensu da suka kawo a jahar Sakkwato mussaman wannan shiri na ’Albishirin ku!’

“Ofishi na a bude yake don bada dukkan goyon baya don ganin wannan shiri ya samu karbuwa a jahar Sakkwato.” jawabinta kenan a wajen taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *