Spread the love


A kowace rana ba abin da wasu nutane ke yi da ya wuce neman farinciki faɗi tashinsu ina za su samu farinciki su dai duk a ƙarshenta dai ko su samu farincikin da suke nema ko baƙinciki ya same su.Mine ne farinciki a rayuwar mutum?Farinciki wani abu ne da ke samun mutum da yake zuwa wurin masoyan  mutum na gaskiya, wasu naganin ba haka ba ne.Farinciki abu ne da yake samun mutum a rayuwarsa wanda shi ne rayuwa da zuciyarsa ke muradi. Ana samun farinciki s wurin masoya da ‘yan uwa da abokan hulɗa ta hanyar a furta kalamai ko ido ya ga abin da ake so ko kunne ya ji abin muradi.Managarciya ta ji tabakin mutane kan abin da suka fahimta da farinciki.Yusha’u Muhammad ya ce farinciki a zuciya yake mutum ya samu kwanciyar hankali sosai ko ya ɗan samu daidai gwargwado”Nutsuwa ke haifar da annashuwa, wadatuwa, soyayya, kulawa da gamsuwa da kuma duk wani abin buƙata na rayuwa. Farinciki shi ne jigon komai. Kuɗi da mulki ba sa iya ba da farinciki.”a cewarsa.Farinciki ne zai sanya ka zauna cikin kwanciyar hankali da lafiya ga jikinka da zuciyarka ta haka za ka so kanka da ƴan ueanka.Hadiza Muhammad a kano take da zama farinciki shi ne rashin damuwa kan komai. Gamsuwa kan komai shi ne farinciki ba nuna ɓacin rai ko hita hayyaci ba.John farinciki shi ne samun gamsuwa da abin da kake yi daga cikin abubuwan da ka samin farinciki kuɗi da bautar ubangijina, in ba kuɗi rayuwa na tawaya, in ba ka tare da ubangiji ma rayuwa ba ta da amfani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *