Spread the love

KUNGIYAR AGAJI TA KASAR QATAR ZATA GINA MASALLATAI DA FAMFUNA A JIHAR YOBE.
.
Comrade Murtala ST
.
A Yammacin Yau Juma’a 14-09-2019 Mai Girmah Gomnan Jihar Yobe Alh. Mai Mala Buni Yagana Da Dr. Hamdi Elsayed Dake Zaman Babban Daraktan Kungiyar Bada Agaji Ta Kasar Qatar A Najeriya Inda Suka Tattauna Kan Yadda Kungiyar Zata Taimakawa Jihar Yobe.
A Yayin Ganawar Tasu Dai, Kungiyar Ta Amince Zata Kina Masallatai Da Kuma Cibiyar Samar Da Ruwa (Borehole) A Dukkan Kananun Hukumomi 17 Dake Fadin Jihar A Matsayin Sadaka Fisabilillahi.
A Yanzu Haka Dai Kungiyar Tayi Ire-Iren Wadannan Ayyukan A Jihohi 8 A Najeriya Wadanda Suka Hadar Da Jihar Bauchi, Cross River, Taraba, Sokoto, Borno, Da Kuma Niger, Duk A Kokarinta Na Tallafawa Addinin Musulunci Da Rayuwar Al Ummah.
Sannan Yasake Bayyana Cewa, Nan Gaba Kadan Kungiyar Zata Duba Yiwuyar Sake Gina Masallatai, Makarantu, Da Sauran Ayyukan Taimakon Al Ummah A Jihar Yobe Kamar Yadda Yanzu Yake Gudana A Jihar Niger.
Anasa Bangaren, Mai Girmah Goman Jihar Yobe Yayi Jinjina Da Godiya Tare Da Sanya Albarka A Wannan Kungiya Da Kuma Shugabinin Kasar Qatar Bisa Namijin Kokari Dasuke Wajen Taimakon Addinin Musulunci Da Bayin Allah A Dukkan Sassa Na Duniya.
.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *