Spread the love

Jam’iyar APC a jihar Kebbi ta ce ƴan takara mutum 800 suka nuna sha’awar tsayawa takarar neman kujerun ciyamomi da kansiloli a ƙananan hukumomi 21 na jihar Kebbi, a jam’iyar APC kawai.

Zaɓen da za a gudanar 26 ga Okotoba Mai magana da yawun jam’yar Sani Dododo a magana da manema labarai ya ce daga cikin 800 ɗin 300 takarar ciyaman suke yi 500 kuwa suke neman kujerun kansila.

Jam’iya ba ta tsayar da kowa ba masu kiran kansu an bar su hamyya ba gaskiya ba ne.

Jam’iya na da tsari na tsayar da ‘yan takara an kafa kwamiti da zai sasanta da yan takara a yankuna shida na jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *