Gwamnatin tarayya ta bakin ministan kudi Hajiya Zainab Ahmad ta ce daga watan Satumba na wannan shekarar gwamnatin tarayya za ta fara rage bashin da take biyar jihohin Nijeriya 35 ga kudin suke karba.

Gwamnatin tarayya ta ba su kudin a 2015 da 2016.

Shugaban kasa Buhari ya umarci babban bankin kasa ya baiwa jihohin biliyan 641 domin su biya bashin albashin da ake biyarsu kowace jiha ta karbi biliyan 17.5.

Lokacin da za a dauka kafin biyan kudin an yi masa gyaran fuska.

Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin da zai karbo kudinta.

An yi yarjejeniya za a biya kudin cikin shekara 20 a kowane wata za a cirewa jiha miliyan 73, har abiya kudin gaba daya.

Daga wannan watan na Satumba gwamnati za ta fara cire kudin. kamar yadda Minista ta fadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *