Spread the love

Daga Jamilu Sani Rarah Sokoto.

Shugaban majalisr koli akan lamurran addini Sarkin Musulmi Alh Saad Abubakar III ya nuna bacin Ransa Game da Abinda Gwamnan Rivers Wike ya yi na rushe masallaci.

A cikin wani jawabi da kakakin majalisar koli akan harkokin addinin musulunci, Farfesa Salisu Shehu ya yi, ya bayyana cewa rushe kowane irin wurin bauta, majami’ar coci ce ko kuma masallaci, abu ne da kan iya ja a hukunta duk wanda ya aikata haka, sannan abune da ba za a lamunta da shi ba.

Haka Sarkin Musulmi ya ce, “muna kan binciken yadda abin yake, idan majalisar ta gama binciken kuma za ta dauki hukunci da ya dace. Domin rushe kowane irin wurin bauta yakan iya janyo fada da tashin hankali a cikin al’umma”.

Har wayau Sarkin Musulmi ya bukaci al’ummar Musulmi da su rika hakuri su daina daukar doka a hannunsu.

Haka kuma Sarkin musulmi ya bukaci shugabanni ‘yan siyasa, sarakuna, malamai da kungiyoyin addini da su hada kai wuri daya su daina yin ko yada abinda zai kawo tashin hankali a cikin al’ummah.

Daga karshe Sarkin Musulmi ya tabbatarwa al’ummar musulmi akan su yi hakuri majalisar na kan bincike kuma da iznin Allah komai zai daidaita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *