Spread the love

Yau take Tasu’a ko gobe?
Mansur Sokoto.

Bismillahir Rahmanir Rahim
Ban dauka cewa, za a samu wata matsala a wannan karon game da watan Muharram ba. Domin gamayyar kwamitocin ganin wata na kasa sun tabbatar ba a samu wani rahoto na ganin wata a Najeriya ba a ranar Jum’ah 29 ga Dhul Hajji. Bisa ga haka, mai Alfarma Sarkin Musulmi ya amince da ranar Assabar ta zama cikon 30 ga Dhul Hajji, lahadi kuma daya ga Muharram. A kan haka, yau lahadi 8 ga Muharram, gobe litinin ce Tasu’a, talata Ashura. Amma abin mamaki tun da asuba kira bayan kira ake ta yi daga ko ina a fadin kasar nan har da makwauta ana ta tambaya da bayyana wasu ra’ayoya masu nuna sabani. Abinda ya kawo wannan shi ne bambancin lissafinmu da na Saudia. Don haka nake son in kara haske kamar haka:

  1. Ba dole ne a kowane wata mu yi daidai da Saudia ba. Idan da mu ne muka gani ba zasu bi mu ba, alhalin mun fi su cancantar ganin wata idan ya fita tunda mu ke yamma.
  2. A irin Sallar layya saboda haduwar ibadu na duniya da yawan Malamai suna ba kasashensu fatawa su bi Saudi Arabia saboda ayi Arafa da layya tare. Mu ma nan Najeriya ana haka, amma wannan ba dole ne ya kasance ga kowane wata ba.
  3. Lallai in da Saudi Arabia za ta jagoranci kasashen duniya su rika amfani da ganin wata guda daya, ita ma ta saurari sauran kasashe ta yi aiki da ganinsu da yawan Malamai za su aminta da wannan don yana tabbatar da manufar Shari’ar Musulunci ta haduwar kan Musulmi a ibada.
  4. A nan Najeriya babu wanda yake da hakken a sanar da shi an ga wata ya amince ya shelanta ma Musulmi in ba Sarkin Musulmi ba, domin shi kadai ne wanda al’umma ta hadu a kan sa.
  5. Wanda ya yi azumin litinin da talata ya dace da 9 da 10 ga wata a Najeriya, 10 da 11 ga wata a Saudia. Kuma duk malamai sun tabbatar wanda ya yi kowannensu ya dace da muradin Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam na sunnanta azumin Tasu’a da Ashura, wanda shi ne azumtar Ashura tare da yi masa rakiya da wani azumi domin saba ma Yahudawa.
  6. A kowane lokaci nikan tuntubi abokaina a groups daban daban da suke kunshe da kasashe masu yawa a ciki, abinda yake ba ni haushi shi ne kowa yana sanar da kwanan watan kasarsu a cikin gamsuwa da amincewa; babu mai alakanta nasu gani da na wata kasa musamman Saudia in ba mu yan Najeriya ba.
  7. Na sha yin bayani cewa, Shari’a tana mayar da lamurra irin wadannan ga shugaba ne ba tare da la’akari da zaman sa na kirki ko akasin haka ba, a’a sai dai kawai don bukatar hadin kai. Ko shakka babu ga wanda ya san shugabannin Musulmin duniya ya san namu jagoranci yana cikin masu kamantawa da tsentseni tare da tantancewa da nuna tsoron Allah a cikin wannan lamari.
    Ina rokon Allah ya hada kan Musulmi a kan daidai, ya ba mu ikon tsayawa inda aka tsaishe mu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *