Spread the love

Shirin bukin auren ya kankama sosai a jihar Zamfara

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya shirya tsaf domin aurar da samari da yan mata tare da zawarawa har guda Dari a Karon farko….

An tsara Yan mata da zawarawa Dari tare da samari dakuma Gwauraye suma guda dari….

Gwamnati zatayi kayan daki tare da dukkan kayayyakin da amare ke bukata, sannan a hada musu da kayan sana’a, su kuma angwaye zaa basu jarin tafiyar da sana’a dukkanninsu, bayan kayan angwanci da zaa dinka musu har da hula da takalma tare da turare….

Gwamna Matawalle yace wannan shine karon farko inda zaa cigaba da kara yawan wadanda zaa aurar lokaci zuwa lokaci

Muna fatar Allah yasa Itama Gwamnatin Jihar Kebbi da Yan siyasarmu da masu hannu da shini Suma sudauki irin wanan tsarin ajiharmu ta Kebbi don rage Zinace Zinace dasukazama Ruwan dare acikin Al’umma..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *