Spread the love

Gwamnatin Jihar Zamfara ta kammala Bukukuwan cika kwana dari 100, a karagar Mulki.

A yau Jumma’a Gwamnatin jihar Zamfara ta kammala Bukukuwan cika kwana dari a karagar mulki, bikin ya kammala ne tare da hawan Daba da kuma kaddamar da Motoci ga jami’in tsaron dake sassan jihar Zamfara domin kara karfin Gwiwar cigaba da tabbatar da tsaro a fadin jihar.

Gwamnan jihar HE Dr. Bello Muhammadu Matawallen Maradu ne yayi jawabin gaban dumbin Al’ummomin jihar inda yake cigaba da zayyano nasarorin da Gwamnatinshi ta samu, wajan habaka tabbatar da tsaro a fadin a jihar kamar yadda yayi alkawarin cikin kwana dari 100 natsalar tsaro ta kau inshaAllahu wajan sace-sacen al’umma da garkuwa dasu.

Haka kuma ya tabbatar da nasarar samar da motocin daukar marasa lafiya da a dukkan manyan asibitoci dake fadin jihar nan take gasu kasa an gani, haka yayi tabbatar da an biya ma’aikatan nan 1400, wadanda Tsohuwar Gwamnati ta Dauka aiki ta kasa biyansu, inda aka tantance fiye da dubu daya aka biyasu.

Haka ya tabbatar da Al’ummar jihar ya samar da takin zamani kamar yadda aka gani nan take gidan taki na jihar ya fara aiki nan take, don amfanin manoma, da kuma samar da hanyoyin kasuwanci fon tallafawa ‘yan kasuwa da koyawa matasa sana’oin hannu kamar yadda yayi alkawari ya bada tallafin kudin naira dubu ashiri ga mata a ko wanne wata, haka ya cigaba da zainno nasarorin da Gwambatinshi ta samu nan take cikin kwana 100, zamfarawa sun gani a kasa yau jihar Zamfara kowa ya sheda an samu canji mai ma’ana.

Ya kara da cewa mun bada aikin gina katafaren filin jirgin sama a nan birnin Gusau, da kuma gina 3Star Hotel da mukayi hadin Gwiwar da wasu masu son kawo cigaba a jihar, kuma gina sabon gidan Gwamnati da muke da kudirinyi ann take.

Fatarmu dai Al’ummar jihar Zamfara ku amfana da tattalin arzikin jiharku rahma ta sauka, duk wani mai kishin jiha ya shigo ya kawo tashi gudunmawa ko waye kofa abude take ta Gwamnatocinmu in dai cigaba zaka kawo mana, muna godiya ga dukkan Zamfarawa dukkan abokanmu da masuyi mana fatar alkairi. Mun gode

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *