Spread the love

Bello Sharada.

Ranar Litinin da ta gabata aka wayi gari da rigima kankanuwa ta sabani ta shiga tsakanin wani mutumin Afirka ta kudu da wani dan Najeriya. Nan da nan sai ta zama tashin hankali da kashe-kashe da kona dukiya.

Abin da ya fi tada hankalin mutanen Najeriya shi ne bidiyon da aka rika yada wa wanda ake nuna wani bakin fata dan kasar waje ana gallaza masa daga karshe aka hallaka shi.

A sanarwar da Magajin Garin Johannesburg ya bayar, wacce ta yi daidai da abin da ministan harkokin ‘yan sanda da kasar ya fada shi ne zuwa yanzu an kashe mutane biyar kuma ana tsare da mutum 189.

Wannan ba shi ne karon farko ba. Tun shekarar da Turawa ‘yan kama-wuri zauna suka mika wa bakaken fata ragamar mulkin jama’a a kasar South Africa a 1994 babu lardin kasar ko wani yanki da a cikin shekarun nan bai yi fama da kisan kabilanci da tashin hankali ba.

Mutanen kasar Afirka ta Kudu bakake ne irinmu ‘yan Africa. A jere Najeriya tana yamma, irinsu Kenya suna gabas. Amma da Zambia da Zimbabwe da Lethoso da Angola da Malawi duka suna kudancin Africa. Wadannan kasashen suna makwabta da Afirka ta KUDU. Najeriya ta ninka South Africa a yawan jama’a sau hudu. Basu fi mutum miliyan 50 ba. Suna da kabilu da al’adu kala-kala.

Kafin kasar Afirka ta kudu ta samu yanci, wadanda suka mulki Najeriya tun daga 1960 har zuwa 1994 sun taka muhimmiyar rawa wajen kwato su daga hannun Turawa. A sanadin haka ne ma CIA suka yi kutunkutun aka kashe Janar Murtala Ranar Muhammad. Ma’aikatan Najeriya sai da suka bayar da kashi biyu na albashin su da sunan Mandela Tax duk don tausaya wa ‘yan uwansu bakake. Yadda aka rika saka sunan Saddam a 1990, haka aka rika sanya sunan Mandela a shekarun 70s da 80s.

Gargajiya da maguzanci shi ne addininsu. Mutanen Afirka ta kudu sun hada da fararen fata Turawa da Indiyawa, Marigayi Ahmed Deedat, dan Afrika ta kudu ne, sannan kuma sai kabilun asali. Irin wannan banbamci na kabila ya sanya harsuna goma sha daya ake amfani da su a harkar gwamnati, saboda kowacce kabila nata harshen take so ya zama a sama. Sun fi son Turanci a matsayin yaren kasa na kowa da kowa.

A South Africa mata ne suke fita aiki da kasuwanci.A cikin kashi 100 na mazan, 28 basa yin aikin komai. Akasarin maza suna gida zaman kashe wando da shan giya da caca. South Africa kasar holewa ce, domin gidajen magajiya da dakunan sinima da wurare na masha’a sune suka fi makarantu da ma’aikatu yawa. Duk wata fitsara da ake yi a sauran sassan duniya ana samunta a Afrika ta Kudu. ‘Yancin duk da ka same shi a Turai ko Amerika zaka same shi a can. Matasan su suna da talauci da lalaci da jahilci. Ana yi wa kananan mata fyade, da wahala yarinya ba ta kai 16 baka same ta an taba yi mata ciki ba. Kisan kai abu ne mai sauki. A South Africa duk bayan awa uku sai an kashe mace.

Duk da haka ‘yan Najeriya suka dauki gammo suka dora a ka, niki-niki a shekarar 1994 suka tafi Afirka ta kudu. Wasu neman karatu, wasu neman harka, wasu kuma aikata mugun laifi. Nelson Mandela ne da kansa ya roki bakaken fata su zo kasarsa su kawo musu alheri, a taya su gina kasar bakake. A lissafin da jaridar Guardian ta fitar daga ofishin jakadancin Najeriya a Afirka ta kudu akwai mutanen Najeriya dubu 24.

‘Yan Najeriya manya irinsu Atiku Abubakar da Peter Obi da Aliko Dangote da T Y Danjuma da Abdusamadu Isyaka Rabiu suna da dukiya mai tarin yawa da suka zuba. Suma ‘yan kasar Afirka ta kudu suna da manyan kasuwanci a Najeriya, DsTV da MTN da Shop rite da hannayen jari a NSE. Akwai malaman jami’a da manyan ‘yan fim da rawa da waka, akwai ‘yan Najeriya masu harkar coci a can. A kananan kuma akwai Inyamurai da Yarbawa da yawa ‘yan iska kwarai, cikakkun masu aikata laifi da miyagun ayyuka. ‘Yan harkar kwaya da yahoo yahoo. Wasu bakaken fata na sauran kasashen kamar Zambia da Zimbabwe da Malawi duka suna da tarin dukiya, wannan dukiya ta tsone wa su bakake na South Africa ido.

A gefe daya duk duniya tana kallon ‘yan Najeriya a macuta, sannan ga tasirin fina finan Nollywood, a daya gefen kuma bala’in rayuwa da zamantakewa da ta addabi matasan South Africa, don haka su a gurinsu miyagun ayyuka da ake aikatawa a kasarsu da kwace musu mata da hana su damar arziki baki ne, kuma ‘yan Najeriya. Suna daukar ‘yan Najeriya kamar Yahudawa. A wajensu ‘yan Najeriya sun lalata kasarsu da laifuka sun zo South Africa zasu bata ta.

Mutanen Afirka ta kudu suna kishin kasarsu, kuma suna kokarin ginata. A ganinsu so ake yi a karya musu kasa. Muma anan gida mu dawo da kishin kasarmu, mu ginata mana. Ba shike nan mun huta da wulakanci da hantarar mu da ake yi a ko ina a duniya ba?. Mai zai hana mu gyara halinmu, sannan mu gyara kasarmu.? Abin takaici a kasar waje a kashe mu, a gida mu rika kashe kanmu. Haba, bayin Allah!

Za a dauki lokaci mai tsawo nan gaba kafin a shawo kan wannan matsalar. Shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi kokarinsa, amma haka zai tafi ya bar wannan musibar. Kone dukiyar South Africa da sace ta a nan Najeriya ba abin da zai haifar, hasali ma gurgunta kasarmu zamu yi da kanmu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *