Spread the love

Kotun sauraren kararrakin zabe dake Sokoto ta yi watsi da shari’ar da aka shigar domin kalubalantar zaben Sanata mai wakiltar Sokoto ta kudu Shehu Abubakar Tambuwal na jam’iyar APC.

Sanata Ibrahim Danbaba Dambuwa dan takarar jam’iyar PDP a zaben da ya gabata ya sanya karar kan zargin an sabawa dokokin zabe, kuma Tambuwal bai samu mafi rinjayen kuri’un da doka ta aminta da su ba.

Haka kuma Tarabunal din ta kori shari’ar da ake kalubalantar dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Kebbe da Tambuwal Alhaji Bala Kokani na APC.

Shari’ar wanda ya gada Abdussamad Dasuki na PDP ya shigar kan aringizon kuri’u da tursasa masu jefa kuri’a da sabawa dokin zabe.

Wata mai kama da wannan kuma shari’ar Kabiru Marafa Acida na PDP ya shigar na kalubalantar Ibrahim Almustafa na APC ita ma an yi waje da ita. Kotun ta ce masu kara sun kasa bayyana gaskiyarsu karara yanda babu kokonto.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *