Spread the love

Wani abin tashin hankali ya faru ga wasu iyali in da aka dauki gawar mutum bakwai da mace mai juna biyu data bakunce su a daki daya a jihar Lagos.

Lamarin ya faru kan titin Olowora, Mafoluku, Oshodi, a Lagas unguwar ta rude kan faruwar lamarin.

A tabakin wani makwabcinsu da ya nemi a sakaya sunansa ya ce Miji ne da matarsa Owojobi da Aminat Sakari da yansu da bakuwarsu mai juna biyu da ake kira Wasilat suka rasu a dare daya, bayan sun kunna Janareto bayan tagarsu.

Ya ce mutanen musulmai ne sun fitowa sallar Asuba bayan karfe 8am ba a ga sun fito ba sai aka damu, aka yi ta kwankwasa kofa ba su bude ba, sai aka kira ‘yan sanda aka buge kofar sai aka samu wasu sun mutu wasun kuma da saura aka kai su asibiti.

Mutum bakwai da mai cikin ne suka rasu kan shakar hayakin Janareton da suka yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *