Spread the love

Gwamnatin Jihar Zamfara karkashin jagorancin Bello Matawallen Maradun ta’aza harsashen gina Rugagen Fulani a faɗin jihar

Aza tubalin an yi shi Runji a karamar hukumar Maradun

A cikin bukukuwan kwana ɗari 100 da Gwamnatin mai girma Gwamnan jihar Zamfara ta yi.

A yau aka ɗora harsashen gina tubalin Rugagen fulani da Gwamnan jihar ya kaddamar ( His Excellency Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradu Barden Hausa) tare da kamawar babban bakonsa gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal

Gina Rugagen dai yana cikin kudirin Gwamnan jihar na tabbatar da alkawaran da yayi na zai ginawa fulani dakunan kwana dari biyar 500 da kuma dakunan duba lafiyarsu, da kuma wajan kiwon dabbobin fulani a ko wanne yanki ukku a fadin jihar Zamfara.

Saboda kara tabbatar da tsaro da Kuma bunkasa tattalin arzikin jiha.

A wajan aza harsashen Gwamnan ya godewa Al’ummomin jiha da goyan bayan da suke bashi wajan kara tabbatar da zaman lafiya da kara yalwantuwar arziki a fadin jihar Zamfara. Taron ya samu halartar Gwamnan jihar Sokoto, da mataimakin Gwamnan jihar Zamfara da shugaban majalisar dokokin jiha da kuma uwayenmu sarakuna da sauran ardo-ardon fulani da mukarraban Gwamnati da ‘yan siyasa a Dajin gidan Ranji dake karamar hukumar Maradun.

Gwamnan ya ce yin Ruga zai kara kawo Fulani kusa da mutane rayuwarsu ta kara infanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *