Spread the love

‘Yan Najeriya za su kauracewa kayan Afirka ta Kudu

‘Yan Najeriya da dama sun dade suna ce-ce-ku-ce da kiraye kiraye kan kauracewa amfani da kayayyakin Afirka ta Kudu sakamakon kin jini da wasu ‘yan Afrika ta Kudun ke nuna wa ‘yan Najeriyar da sauran kasashe mazauna can.

Akwai kamfanonin Afirka ta Kudu da ke zaune a Najeriyar kamar kamfanin sadarwa na MTN da kuma shagunan siye da siyarwa na Shoprite da kuma kamfanin talabijin na DSTV.

‘Yan Najeriya da dama na ci gaba da kiraye-kiraye a shafukan sada zumunta musamman Twitter da Facebook inda suke nuna bacin ransu kan yadda wadannan kamfanonin mallakar Afrika Ta Kudu ke samun kudi da ‘yan Najeriya, amma wasu ‘yan kasar ke nuna kin jini da kuma kai hari ga ‘yan Najeriya mazauna kasar.

‘Yan Najeriyar na amfani da shafin Twitter da Facebook da kuma wasu shafukan sada zumunta wurin bayyana ra’ayoyinsu da kuma kiraye-kiraye na kauracewa kamfanonin.

Wani kenan a shafin Twitter yake cewa ya kamata mu kauracewa kasuwancin Afirka Ta Kudu a Najeriya kamar DSTV da MTN da wasan Big Brother da ake nunawa a talabijin da kuma kantin sayar da kayayyaki na Shoprite.

Sai dai akwai wasu da ke nuna cewa daukar mataki kan kamfanonin ba zai sauya komai ba.

Wannan kuma na cewa asalin masu manyan kamfanonin da ake kira a kauracewa ba asalin ‘yan Afrika Ta Kudu ba ne, Turawa ne.

Tuni dai gwamnatin Najeriya ta aike wa jakadan Afirka Ta Kudu a kasar sammaci kan hare-haren kin jinin baki da ake kai wa ‘yan Najeriya a kasar.

Ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama zai gana da jakadan Afirka Ta Kudu a ranar Talata kan kashe-kashe na baya-bayan nan da aka fara a karshen makon nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *