Spread the love

Hanyoyin Adana Harshhe da Al’ada a Gargajiyance ll

Farfesa Salisu Ahmad Yakasai

Cigaban fitowa ta biyu:

Wakokin da yara ke yi sun hada da: Ina da cikin dan fari, da Wee Ni kura, da Carmandudu-carmanduduwa, da Dokin naka kuru ne, da Malam na bakin rafi, da Awoawo, da Jinijini, da Kullikucciya da sauransu. Wato wakokin wata ma’adana ce ta amfani da harshe da zabin kalmomi cikin wasanni. Wadanda mata ke yi kuwa cike suke da kalmomin Hausa da salo da kuma hikima, musamman ma idan aka yi la’akari da cewa suna bijiro da batutuwa daban-daban na zamantakewa da kuma wadanda suka shafi al’umma gaba daya. Haka kuma wakokin da wasannin suna bunkasa hikima da basira cikin azanci da lissafi kamar: Malam na bakin rafi da kulli kucciya da Ina da cikin ]an fari. Wa}o}in Awo da Jinijini suna adana harshe da kuma na}altar magana, wato a inda ake sanya yaro ya jajirce cikin fahimtar ma’ana a }ananan shekaru. Ita kuwa wa}ar Awo tana koyar da fahimtar nau’i daban-daban na hatsi a al’ummar Hausawa, ita kuma ta Jinijini tana koyar da sanin dabbobi ne daban-daban.

Akwai kuma kacici-kacici da wasa }wa}walwa da kuma wasa da harshe. Su ma wa]annan akan su wani madubi ne na kallon rayuwar al’umma da kuma kafa ta adana harshen Hausa da al’adun Hausawa. Galibi sigarsu a magance suke bijirowa, kuma manufarsu ita ce bun}asa basira da tunani. Shi kansa harshen kacici-kacici da na wasa }wa}walwa, rumbu ne na adana kalmomin Hausa daga zamani zuwa wani, da kuma zubi da tsarin harshen Hausa. Ana ganin tsarin harshen ne daga hikimomin da yara da manya kan na}alta. Su kacici-kacici da wasa }wa}walwa suna }umshe ne da tambayoyi da aka tanada domin kaifafa hikima da basira cikin fahimtar ma’anar kalmomi da sassan jumla. Ga misali, wasu tambayoyin na wassafawa ne, a yayin da wasu kuma na amsa-kama da na magance matsala tare da hujja da dalili. Ga sigar yadda suke bijirowa:

                  Tambaya: Ta}anda ba }ashi ba?

                  Amsa: Kanwa

                Tambaya: Baba na ]aka, gemu na waje?

                Amsa: Wuta da haya}i

                Tambaya: Shanuna dubu ma]aurinsu ]aya?

                Amsa: Tsintsiya

                Tambaya: Kurkucif-kucif?

                Amsa: Kwanciyar kare

Abin da ya fi ban sha’awa dangane da adana harshe, shi ne na wasa da harshe. Wato a nan ne ake nuna }warewa cikin na}altar tsarin harshen Hausa. Akan }ir}iri wasanni daban-daban da suka ta’alla}a ga harha]a sautuka ko ga~a ko kalmomi. Galibi wasannin kan }unshi maimaicin sautuka masu kama da juna, amma kuma masu wuya ko wahala wajen furtawa. A wasu lokuta kuma sukan }unshi tsarma sautuka ko kalmomi tsakanin ga~a ko kuma tsakanin kalmomi da ke cikin jumla. Haka kuma sukan bijiro a siga ta zaurance da karya harshe ko }arangiya da kuma tunku]a bami. Baya ga adana harshe, wa]annan wasannin gargajiya suna kuma adana kyawawan halayen Hausawa, wato suna }unshe da tsarin zamantakewar Hausawa da suka danganci siyasa da tattalin arzi}i da addini da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *