Spread the love

Hajiya Kulu Abdullahi babbar diya ce ga shahararren manomin nan da aka sani a kasar nan waton Ali Namani Kotoko, kuma ita ce mataimakiyar magatakardan jami’ar Usman Danfodiyo ta Sokoto, noma da aure ba su hana mata yin karatun boko mai zurfi ba. Ta kuma yi nasarar gadon mahaifinta.

Tarihinta:

Sunana Kulu Abdullahi an haifeni 24 ga watan 4, 1963 a garin Wasagu maifina margayi Ali Namani  Kotoko sanannen manomi ne a kasar nan ta Nijeriya ni ce ta fari wadda Allah ya kaddari ta tsaya, a lokacin muna yara ba’a san kabilanci ba irin wanda ake yi yanzu, abin da yasanya anka  kai ni yaye a wurin wata Bayarbiya aminiyar mahaifanmu Allah bai ba ta haihuwa ba, ta nemi izini ga mahaifana za ta je dani garinsu na Ogmosho mun kawo wani gari Bade muka yi hadarin mota ta rasu abin da ya mayar dani wajen mahaifana, na dawo ban jin Hausa kwarai a haka aminin mahaifina ya ce a sanya ni makarantar boko don in na yi hulda da yara yan uwana zan iya Hausar da aka sani karatun kuwa ya mike in da har na yi karatun Firamare na shiga Sikandare kwalejin mata  a 1975 a garin Tungar Magajiya na kamala shekara biyar don a lokacin su ake yi, na yi digiri a jami’ar Usaman Danfodiyo a fannin Tarihi. Na yi aure na auri Malam Audu Zuru a yanzu Farfesa wanda shi ne ke shugabantar Jami’ar Danfodiyo a yau. Na samu aikin gwamnati tun ina bautar kasa a lokacin aiki baya wuya na fara da karantarwa a 1986, bayan dawowa daga kasashen waje ni da mai gidana na koma gidan waya da aiki, dana yi shekara shida a wurin sai na koma jami’ar Danfodiyo da aiki in da a yanzu nake mataimakiyar magatakardan jami’a(deputy registar).

Kalubalen da kika fuskanta:

Kaluballe suna da yawan gaske na farko yanayin rayuwa a matsayina na ma’aikaciya za ka abin da kake samu ba zai isheka har ka taimaka wasu  ga  tarnaki a wurin gudanar da lamurranka. Zamana na mace ma ya sanya na samu kalubale a yanayinmu na addini da al’ada, musulunci ya shata yanda mace za ta yi hulda amma al’ada tana hana mace cimma burinta don nima kaina al’adar ta hanani don karatun shari’a na so yi. Noma da nake sha’awa in mace tace za ta yi shi sai a dauke shi wani abu ne daban ka ga ka ga kalubale ne.

Burinki na rayuwa na gaba:

Ina son mata su gane sana’ar noma ba ta maza kadai ce ba in dai har mace za ta iya tafiya kasuwa da wurin buki banga dalilin da zai sa ba za ta je gona ba, sana’ar noma harka ce mai albarka fiye da yanda ake zato, ba dole mace sai ta je ta zauna a gona ba, ina baiwa mata shawara su koma gona shi zai sanya yaranmu su koma, duk abin da suka ga muna yi shi za su yi in sun yi shi zai sa su tashi cikin sana’a.

 Sha’awarta ga harkar noma:

Da muka fita kasar waje da mijina na dakatar da noma bayan mun dawo daga Turai sai na gayawa mahaifina ina son na koma noman Sai yake ce min Kulu noma ba naki ba ne lokacin ban fahimce shi ba sai daga baya don gwamnati ba ta taimakawa manoma ba su da kwarin guiwa zaka ga manomi ya yi noma ba riba sai hasara ba a baiwa bangaren muhimmanci komai kai zaka samo abinka dole Ka samo Shi cikin tsada, in za ka sayarwa ka samu nasara kasashen waje yafi naka arfa da tsafta da Kyau don sun fi gyarawa, a lokacin da na dawo noman mahaifina baya da lafiya bayan ya rasu ne 2014 muka debe amfanin gonar da muka shuka noman ya zamar muna hasara sosai, da wata shekara ta zo kanena suka ce mu bar noman nace ba zai yiwu ba sunan da mahaifinmu ya yi cikin noma da yanda yake sonsa cikin zuciyarsa kuma ya fada mana ko bayan ransa mu rike noma sana’a da muka cigaba ne muka yi sa’a gwamnati ta juyo kan harkar sai na tabbata noma sana’a ce duk abin da za ka yi ka ci riba ba kamarsa na cigaba da noma ne don ina son sunan mahaifina kar ya mutu a manta da shi kuma na rike ne don Sabo da shi bayan kasuwanci.

Sirrin shahararki a noma:

Kar ka manta mahaifina shahararren manomi ne na fara taka sawunsa, kafin na cimmasa akwai aiki don muna da banbanci da shi, ya yi noma ne Saboda suna, mu ko muna yi ne Saboda riba dole ne mu kula da wasu abubuwan da dama akwai aiki. A maganar shahara kuwa a gaskiya ina ganin abin da ya burge mutane a sharata a Kebbi bai fi zamana mace ba na tabbata akwai manoma da ban taka kafarsu ba amma dai suna mamakin yanda mace ke noman da nake yi a shekarar data wuce na samu buhun masara da Dawa 259 a wata gona kuma 522 ban samu shinkafa ba don buhu 15 Kawai na yi sabanin 32 dana samu a wata shekara, gona kuma ina noma mai hekta 18 da mai 102 dana gada a wurin mahaifina da fadama mai hekta 52  a duk sanda za mu fara aikin gona bayan masu gadi mukan dauki mutum 50 don shuka noma da sanya taki a sabon salon da muke amfani da shi mutum ashirin zuwa da biyar sukan yi fiye da kwana 10 suna aiki haka a girbi huldar tana da Kalubale Saboda ba mu da mashin da tasirin yafi haka. 

Kina da shiri na canja tunanin mata su shigo harkar noma gadan-gadan:

Abin da nake fatan gani maza da hukuma su baiwa mata goyon baya a taimaka masu da abin hannu na tallafi in an cire amfanin gona sai a biya da shi ko araba riba. Ina da shirin da zan fito da shi da kudina don taimakawa mata su yi noma a san su ma suna iyawa, yakamata gwamnati ta yi yekuwar mata su yi noma don addini ya baiwa mata damar su yi sana’a sai kuma abasu kwarin guiwa da kulawa don ita ce na samu mahaifinmu ya bar muna baiwar kasa da tarbiya shi ne yasanya mutane ke cewa Namani bai mutu ba. 

Ga shi mun kara samun daukaka gwamnati ta daraja noma a haka muka kara tabbatar muna da sana’a duk da sai a bana ne gwamnati ta San dani ta bani tallafin noman rani na iri da taki da injimin ban ruwa gaskiya shirin tallafawa manoma bai yi tasiri ba sosai daga baya naji an ce Irin Anko baya da Kyau na Alkama kuma ba a ba da shi cikin lokaci ba amma dai ba komai manoma sun koya ne in na samu irin zan shuka shi duk da ina tanadar nawa mai inganci. Ina kira ga nanom a mu kamar yanda muka karbi noma sana’a ne mu karbi canji dake zuwa don gwamnati na nufin mu rika shuka abubuwan waje don dogara da namu mu fita batun na waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *