Spread the love

MATASA MAZA DA MATA YA KAMATA SU SANI HARKAR SHAYE-SHAYE BA TA SU BA CE.

Shahararren dan kwallon kafa na Nijeriya Abdullahi Shehu ya samar da wata gidauniya ta kashin kansa, da za ta rika tallafawa matasa da wayar da kansu kan hatsarin shaye-shaye.

Abdullahi ya yi gangamin wayar da kan matasa in da aka gudanar da tattaki har zuwa babban dakin taro na kasa da kasa dake unguwar kasarawa, taron ya yi armashi an samu goyon bayan gwamnatin jiha da matasa baki daya.

A kalamansa wajen gangamin ya ce matasa maza da mata yakamata su sani harkar shaye-shayen miyagun kwayoyi ba ta su ba ce, su natsu su san abin da ya dace a rayuwarsu.

Irin wannan gudunmuwar ce amatsayinsa na matashi dan jihar Sakkwato yake ganin yakamata ya shigo ya kafa wata gidauniya da za ta rika tallafawa matasan shi ma ya ba da tasa gudunmuwa don gina jiha.

A Cibiyar wasanni da zai samar a Sakkwato tana cikin abubuwan da za su taimaki matasa wurin gina rayuwarsu har su zama abin alfahhari ga al’ummarsu kamar sauran nagartattun mutane.

Gwamnan Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya yi alkawalin gwamnatinsa za ta ware fili ta damka wa matashin domin gina cibiyar kamar yadda ya kudurta.

A lokacin da Shehu ya ziyarci gwamnan a shekarar da ta gabata ya yi masa alkawalin sai dai har yanzu filin bai shigo hannun matashin ba domin soma ginawa, gata anan gwamnati ta cika alkawalin domin wannan abin da zai yi taimakon jiha ne da al’ummarta gaba daya, hakan yana cikin nauyin da gwamnati ta dauka na Samar da aikin yi ga matarsa don kawar da zaman banza.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *