Spread the love

Mai garin Yandaka a kauyen karamar hukumar Batsari dake jihar Katsina Shehu Ilyasu ya samu mummunan rauni, matarsa da diyansa uku an tafi da su a lokacin da mahara suka kawo farmaki a gidansa Assabar data gabata da dare.

Hukumar ‘yan sandan jihar sun tabbatar da faruwar lamarin.

Mai garin an harbe shi da kai da hannu an yi sauri an kai shi asibiti daga baya suka wuce da shi asibitin Aminu Kano don yi masa aiki a kwakwalwa. Kamar yadda majiyar ta ce.

Ya tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun ‘yan sanda Isah Gambo ya ce gaskiya ne an kaiwa mai gari hari an yi garkuwa da wasu diyansa a lokacin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *