Spread the love

 MUHIMMAN ABUBUWA 21 DA AKE SON UWAYE SU YI AMFANI DA SU A WAJEN TARBIYARTAR DA DIYANSU.

MALAMA HADIZA SALKA.


RENO A MUSULUNCI  KAMAR  YADDA MUKA SANI ADDININ MUSULUNCI YA KARANTAR DA MU DUKAN FANNONI   NA RAYUWA  KAN ABINDA YA SHAFI RENO  KAMAR YADA ALLAH YA UMURCE MU A CIKIN SURATUL  TAHARIN AYA TA 5  INDA ALLAH YA UMURCEMU DA MUKARE KANMU DA ‘YA’YANMU DAGA WUTA, ITA WANNAN WUTAR MUTANE DA DUWATSU NE MAKMASHINTA DON HAKA AKWAI BUKATAR KULAWA DA HAKAN.

MA’AURATA SU JI TSORON ALLAH SU TARBIYANTAR DA IYALINSU. TARBIYAR MUSULUNCI, A CIKIN WATA FADA TA MANZON ALLAH (S.A.W) YA CE “DUKANMU MAKIYAYA NE KUMA ALLAH ZAI TAMBAYE MU KAKAN KIYON DA YA BAMU. AKWAI BUKATAR MIJI YA CIYAR DA MATARSA DA HALAT DON SAMUN ZURIYA DAYIBA WACE ANNABI S.A .W ZAI ALFARIDA   ITA RANAR ALKIYAMA. ABUBUWAN DA AKE TSAREWA DON SAMUN INGANTACCIYAR TARBIYA:
1. LOKACIN DA MACE TAKE DA JUNA BIYU ANA SO TA KASANCE MAI YAWAN KARANTA QURANI  SOSAI TA GUJI CIN HARAM 

2. TA KASANCE MAI YAWAITA SALATIN ANNABI S. A .W DAI WANNAN LOKACIN TA LIZINCI  CIN DABINO DA SHAN ZUMA

3.  SANNAN ANSO KADA AYAWAITA BATA MATA RAI 

4. ALOKACIN DA CIKI YA KAI LOKACIN HAIHUWA KUMA ANSO LOKACIN DA NAKUDA TA FARA TA YAWAITA KIRAN ALLAH KADA TA HAIHU WAJE MAI KAZANTA KUMA KADA TA ZAMA ZINDIR  

5. BAYAN AN HAIHU ANA SO A GOGE MA YARO JIKI DA MAN ZAITUN KO MAI, MAI HASKE AMMA KADA MAN YA SHIGA KAFAR ISKA NA JIKIN JARIRI 

6. ANSO UWA TA DAUKI ABINDA TA HAIFA TAYI ADU’A TACE MASHA ALLAH LAKUWATA ILLAH BILLAH 

7. TA FARA BADA NONON DAMA KADA TASHAYAR KWANCE KO TSAYE KUMA TA BADA NONON TANA ABBATON ALLAH 

8. ADUK SADA ZATA DAUKI YARO KO AJE SHI MA, TA ANBACI ALLAH KAaR TA YI LA’AKARI DA CEWA BAYA JI KASANCEWAR SHI YARO KA DA TA MANTA ITA CE MAKARANTA TA FARKO 

9. HAKIN UWAYE NE BA YARO SUNA MAI KYAU MAI TARIHI MACE KO NA MIJI

10. SUNNA CE MAI KARFI YIN ASKI RAN SUNA AMMA ITA MACE ANA YI MATA SAISAYE HAKA KUMA KADA AYI WA YARO TSAGE A JIJKIN  SA  YIN HAKAN HARAMUN NE  MUTUKAR BA NA RASHIN LAFIYA NE BA  

11.  HAKIN MAHAIFIYA NE KULAWA DA YARO DA KARE SHI DAGA DUK ABIN DA ZAI SA YARASA LAFIYARSA A WAJIBI NE KARE SHI  DAGA SANYI ZAFI  MISALI  LOKACIN SANYI A SA MASA KAYAN SANYI   BA KUMA NISANTA DUK ABIN DA ZAISA YA JI CIWO KAMAR WUKA KWALBA   A KUMA NISANTA ABINDA ZAI DAUKA YA CI KO YA SHA YASA SHI RASHIN KAFIYA KAMAR BARAGUNI MAGANIN KUSA DA SAURANSU 

12. AIKIN UWA NE BA YARO ABINCI IDAN ZA TA BA SHI TA FURTA BASMALA YA JI, IDAN SHI ZAI CI DA KAN SHI YA WANKE HANUNSA NADAMA TA TABATAR DA YA YI BASMALA YA CI GABANSA SANAN KADA ABARI YA YI HANU BAKA HANU AKUSHI, A AJE MASA RUWA KUSA  SANAN KAR ABARI YA WUCE WURI WAJEN CI  

13. UWA TA KULA DA TUFAFIN DA TAKE SAMA YARO, ‘YA MACE A  NUNA MATA SUTURCE ALAURATA TUN TANA KARAMA  MA’ANA SA KAYA NA MATA, NAMIJI KO A KOYA MASA SA KAYA IRIN NA ANNABI S. A .W

14 . UWA TA TABATAR DA YARO YA YI BISMILLAH WAJEN SA KAYA, ZAMA, TASHI, KWANCIYA, SHAN RUWA, ANAN MA TA TABATAR DA YA BI SUNNAR SHAN RUWA,, SHA ZAUNE A JA SAU UKKU A DAUKE DON A YI NUNFASHI KADA ABARI YARO YA CI ABINCI MAI ZAFI 

15. HAKIN MAHAIFA NE KOYAWA YARO KARATU DA  RUBUTU  MUSAMAN NA ADDINI DA NA BOKO DON NEMAN DUNIYARSU 

16  AKWAI ADU’AR KARE YARA DAGA ZINA TUN SUNA YARA KAMIN SU BALAGA SAI AYI MASU ITA SURATUL RAHAMAN ZA’A KARANTA SAU 9 SAI  INSAHA ALLAH ALLAH ZAI KARE SU  

17. ANA KARANTA IHIDINAL SIRADAL MUSTAKIN ABA YARA SU SHA NA SHIRIYA 

18. GA MASU SHAYE SHAYE ANA KARANTA SURATUL FATIHA 7 GA RUWAN LEMON TSAMI ABA MAI SHEYE SHAYE YA SHA DA SAFE KAFIN YA CI KOMAI HAR KWANA 7 INSHA ALLAH SHIMA ZAI BARI 

19 CIN DABINO NA TAMAKAWA YARA WAJEN GANE KARATU DA SHAN ZUMA

20. YANA DA MUHIMANCIN GASKE UWA TA NUNAWA YARANTA YIN ASAWAKI KASANCEWAR SUNNA CE TA ANNABI S. A. W 

21. ADUAR UWA DA UBA BA KARAMIN TASIRI YAKE YI BA GA RAYUWAR YARO KAN HAKA UWAYE SU YI ADU’A TA KWRAI GA DIYANSU.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *