Spread the love

Rahoton da Managarciya ta samu ya ce mutanen da aka yi wa haihuwa a Kano ba su da ragon suna, kan tuntubi mahautan da su ke da alaka da su.

Sai su yi yarjejeniyar Sayen hanjin Ragon da za a yanka domin sayarwa. Shi ne kadai na wanda aka yi wa haihuwar.

Daga nan mahaucin kan ba da ragon da yake shirin yankawa domin a sayarwa jama’a danye. Sai a kai ragon gidan da aka yi haihuwar a dare ko ranar suna da safe.

Za a fito da Ragon, a yanka a fede a gyara akan idanuwan mutane, a matsayin ragon suna. Sannan kuma, za a kwashe Kayan Ciki a kai cikin gida a cigaba da suya. Gangar jikin ragon kuwa, akan rataye shi kamar yana jiran suya ko gashi.

Da zaran lokacin fara sana’ar Mahaucin ya yi a dauki gangar Jikin ragon nan a mayarwa da mahauci Kayansa ko shi ya zo ya dauka da kansa kamar zai je gasa ragon a dawo da shi gidan haihuwa, amma shi kenan ya tafi kenan sai abin da mai jego ta gani

Gidan Rediyon Dala FM da ke Kano, a wani shiri mai suna BABA SUDA, ne aka labarta yanda tsarin ba da hayar RAGON SUNA yake ga masu bukata a jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *