Spread the love

Sanannan ‘Yar wasan Hausa Ladidi Muhammad wadda aka sani da mutu ka raba ta karya ta masu fadin tana fama da cutar kansa wadda aka fi sani cutar daji.

Ta ce karya ne ake yi ba ta da cutar daji ta yi rashin lafiyar ne, kuma ta ji dama.

Wadan da suka dauki hotonta a lokacin da take shan iska ba ta sun dauka ba kuma ba ta da masaniyar yaudarar da suka kulla “an ce Wai sun sanya nambar asusun ajiyar banki da sunan a taimakamin kan halin da nake ciki wannan karya ce yaudara ce ba da sani na ba kuma bansan wadan da ke yi ba ka da duk wani masoyina ya tura kudi da nufin a taimakin mayaudara ne”

Ladidi ta yi wannan bayani ne a lokacin da tawagar matan Kannywood suka ziyarce ta domin duba jikinta.

Ciwon sabara ne ya buge ni kuma na samu sauki ba wata Kansa da nake fama da ita, masoyana su sani. In ji Ladidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *