INA GOYON BAYAN SHUGABA BUHARI YA CI GABA DA YA{AR MACUTAN {ASAR NAN—WALIN KALGO.

Bashir Lawal Zakka, Birnin Kebbi.

Malam Abubakar Muhammad Atiku Walin Kalgo shi ne tsohon limamin sojojin Najeriya, yana daya daga cikin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC mai mulkin Jihar Kebbi Da kuma kasa baki daya. A tattaunawarsa da Managarciya ya yi maganganun da suka shafi jihar Kebbi da kasa baki daya.

Managarciya: Me za ka ce game da kafa kungiyoyin siyasa da aka yi a Jihar Kebbi BBSO da 4+4?

Walin Kalgo: Bismillahir Rahmanir Rahim, a matsayina na almajiri na addinin musulunci kuma mai sha’awar siyasa saboda Muhammadu Buhari dattijo nake jam’iyyar APC a Jihar Kebbi, to lokacin da aka yi (two terms) idan ba’a manta ba, lokacin tsohon Gwamna Saidu dakin gari, Allah ya sani Saidu ya sani yana nan da ransa a yanzu da muke maganar da kai, na sami Saidu daga ni sai shi, sai Allah na fada masa a matsayinka na Gwamna uban kowa kana gani yaran nan sun fito da wani abu wanda zai kawo maka mastala, a cikin siyasa a samu baraka, saboda haka ka kirasu ka yi musu alheri kuma kayi godiya ka ce musu su bari, har sai in manyan ‘yan siyasa sun hadu sun tattauna akan kafa kungiyoyin siyasa. Amma Saidu bai yi amfani da Magana ta ba, kuma na yi wa shugaban jam’iyyar PDP na wancan lokacin Marigayi Alhaji Kasimu Baura magana na ce ya kuka bari ana ta bude ofisoshi na kungiyoyin siyasa barkatai. Irin bude wadannan ofisoshi ba zai haifar muna da da mai ido ba, akan irin wannan ne har yanzu a Jihar kebbi muke da bangaranci a cikin siyasarmu, domin alokacin Saidu bai yi amfani da shawarwarin da muka ba shi ba.

Bari in koma ga tambayar da ka fara yi mani, a halin gaskiya su wadan nan kungiyoyi na siyasa da aka kafa anan Jihar Kebbi BBSO da 4+4 ba alheri ba ne, ga maigirma Gwamna Bagudu, na sha zuwa domin in fada masa illolin kafa wadan nan kungiyoyin siyasa amma Allah bai sa mun sadu da shi ba, na fada ma na kusa da shi, su fada masa illolin kafa wadan nan kungiyoyin siyasa domin dukkansu wadan da suka kafa kungiyoyin mutanen ne na kusa da Gwamna kuma duk bukatar su guda ce nasarar Buhari da Bagudu a zaben 2019.

To amma me zai sa abari wasu mutanen banza yan tasha su rika ruruta wuta tsakanin wadan nan kungiyoyi guda biyu har ta kai ana zage-zage da kone-kone da farfasa gidaje da ofisoshi da motoci; misali ka duba irin muhimman mutane masu darajja a Jihar Kebbi takai suna yiwa junansu maganganu maras dadi, naji yadda Sani Zauro Zannan Gwandu ya yi wa Sani Dododo da kuma yadda Sani Dododo yake maida wa wani ]an Argungu martani a cikin kafafen yada labarai, irin wadan nan maganganu na banza bai kamata dattijai suna irin wadan nan maganganu ba, amma idan kai da mutum ne ka zage shi da sauke-sauke amma ka fito cikin kafafen yada labarai kana zage-zage a matsayinka na dattijo bai dace ba, ka karantar da na bayanka kenan kuma ka haddasa fitina, har zuwa ga yan’uwa da abokan arziki, wanda ba’a san ranar karewar ta ba, saboda siyasa.

Managarciya : Me zaka ce game da maganganun da mai ba Gwamna shawara ta harkar siyasa Alhaji Yusuf Rashid yayi akan Faruk Yaro Enabo P.A, wajen babban taron 4+4.

Walin Kalgo: To a halin gaskiya mai ilimi kamarsa kuma dan sarki wanda ya fito daga babban gida kuma jikan Abdullahin Gwandu, wanda yana iya rike wannan gida a halin da muke ciki yanzu. Gaskiya irin wadan nan maganganu da ya yi a wurin wannan babban taro da aka gudanar ba halinsa ba ne, ko shi yanzu da ya yi wadan nan maganganu idan ya tuna da abin da ya fada zai ce ya yi bakin cikin fadin su. Saboda haka muna kira gare shi nan gaba irin wadan nan maganganu bai kamata su rika fitowa daga bakin sa ba, kuma kada wasu ‘yan siyasa su goyi bayan wadan nan maganganu da ya yi, ya tuna fa duk dan kasar Gwandu talakkan shi ne, in dan Sarkin Gwandu ko Jikan  Sarkin Gwandu ya ce baya son wani talakkan kasar Gwandu to ya yi kuskure.

Ina kuma kira ga mu malammai idan muka zo yin wa’azi mu rika fadin kalamai masu amfani ga jama’a ba irin kalamai da za su jawo tashin hankali ba, mu guji haddasa fitina tsakanin ‘yan siyasa dan biyan wata bukatarmu.

Managarciya : Me zaka ce game da korafe-korafen da al’ummar yankin Zuru da Yauri ke yi cewa an barsu abaya musamman wajen na]a mukamai?

Walin Kalgo: su masu  irin wadan nan korafe-korafe sun manta da cewa Gwandu ita ce uwa ga yankunan nan guda uku, kuma a sarautun nan guda uku Argungu da Yauri da Zuru, Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kebbi shi ne Maimartaba Sarkin Gwandu, idan aka ce kai shugaba ne, to kai ne uba kamar Abuja ne da sauran Jihohin Nijeriya, mu dai abin da muke bukata duk daga inda ka fito in dai dan Jihar Kebbi kake to ka nuna halin kwarai a wurin gudanar da aiyukanka kuma ka yi adalci ga kowa ga duk inda mutum ya fito ko Argungu ko Yauri ko Zuru ko Gwandu.

Mukami yana da kyau ga duk wanda ya dace a ba shi ko da kafiri ne, in dai zai yi adalci akan kowa ya halatta a ba shi mukamin, in dai har ya iya aikin kuma in zai ba kowa hakkinsa ana iya ba shi domin musulunci ya yarda, amma mutane abin da ya dame mu shi ne hassada, amma ya za’ace wanda bai cancanci ya rike mukami ba a ba shi, irin wannan ba zai haifar mana da da mai ido ba, saboda haka ina kira ga yan’siyasar Jihar Kebbi mu ba da hadin kai dan ciyar da Jiharmu gaba domin shi ne mafita ba wai yin korafe-korafe akan mukami ba.

Managarciya : To yanzu menene mafita?

Walin Kalgo: Madalla, ga mafita nan,  Sanata Muhammadu Adamu Aliero da Gwamna Bagudu sun zauna sun yi nazari cewa idan abin da ke faruwa ya ci gaba a cikin wadan nan kungiyoyi to jam’iyyar APC za ta samu matsala kuma za’a samu fitintinnu a cikin al’umma saboda haka Sanata Adamu Aliero ya kira taron manema labarai ya ba da sanrwar rushe duk wata kungiyar siyasa wadda aka kafa ta a karkashin jam’iyyar APC, ya ce kuma duk wata kungiyar siyasa wadda aka kirkiro ta a cikin APC yanzu ta koma a matsayin kungiyar jam’iyyar APC, duk sun koma cikin kungiya guda kenan.

Managarciya: Wace shawara za ka ba shugaban kasa Muhammadu Buhari?

Walin Kalgo: Shawarar da zan ba shugaban kasa Buhari ita ce, ya ci gaba da wannan aiki na yaki da mahandama da macuta da suka sace mana kudinmu suka kai wa iyayen gidajen su a kasashen waje. Ina kara kira ga shugaban kasa duk girman mutum ko mukaminsa ko shi wanene idan ya ci kudin al’umma a tursasa ya dawo da su kuma a hukunta shi, su kuma alkalai su ji tsoron Allah su tuna za su koma gaban Allah, ko kai musulmi ne ko kirista za ka mutu, saboda haka muna nan muna ta addu’a duk wanda ya daure wa azzalumi gindi Allah ya tona asirin shi.

Don haka Buhari ya ci gaba da aiki, Allah zai kare shi daga dukkan miyagu, duk masu kulle-kulle ba za su samu nasara ba. Ni ba ma’aikacin Gwamnati ba ne, kuma ba na yi mata kwangila, amma ina son a samu gyara a kasar nan. Gwamnonin APC kuma su ji tsoron Allah su taimakawa shugaban kasa ta fannin tsaro da kuma kama barayin da suka sama da fadi da kudin a’lumma, kuma su fito da shirye-shirye na inganta harkokin al’ummar Jihohinsu.

Managarciya : Me zaka ce ga jama’ar kasa?

Walin Kalgo: Jama’ar kasa su tuna bayan wuya sai dadi, kuma bayan bakin ciki sai farin ciki idan muka tuna a lokacin mulkin Buhari na soja a baya, mun sha wahala a farko, bayan haka kadan komai ya zo ya daidaita, dadi ya zo. Sai daga baya aka kawar da shi aka zo aka mayar da hannun agogo baya, aka ciwo mana ba shi duk da munce bamu so, aka karya mana darajar kudi aka mayar damu bayi. Ga yadda muka iske kanmu a ciki yanzu ta yadda komai ya tabarbare a kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *