Spread the love

“Bana shawan sake fitowa takarar kowane mukami domin duk jam’iyyun manya APC da PDP ba su da lafiya ta a fito takara cikinsu kuma ba su goyon bayan takarar mata a hakikanin gaskiya”.

Hajiya Aisha Garba  Aliyu Gusau ce ta yi wannan furucin a zantawarta da Managarciya a satin da ya gabata don sanin in da ta sanya a gaba siyasa ganin cewa ita sanannar ‘yar siyasa ce Arewa da kasa baki daya. 

 Ta ce har Yanzu ita ‘yar jam’iyar PDP ce tana cikin jam’iyar  amma maganar takarar ce ta janye a yanzu don ko bayan matsalar jam’iyyun akwai ta maza dake danne su, su hana masu rawar gaban hantsi abin da ke ci mata tuwo a kwarya. 

“A 2005 na shiga siyasa na fito neman ‘yar majalisar jiha a Gusau ta tsakiya a zaben fitar da gwani dattawan jam’iya suka roke ni da na janye ba yanda na iya dole na hakura wannan na ci wa mata tuwo a kwarya. 

“Wani abu daban bayan danne mata a cikin tsarin jam’iyya akwai rashin hadin kai a wurin ‘yan uwansu mata ba su ba da hadin Kai su zabi mace, in da maza suka karkata nan suke tafiya, da za mu samu hadin kan mata a kasar nan da za a samu mata a mukaman zabe fiye da yanda ake yau.” Hajiya Aisha Gusau. 

Ta }ara da cewar ta yi shugabar mata ta PDP a kasa baki daya bayan shugabar mata ta Arewa a kungiyar dawo da mulkin Nijeriya a Arewa wadda Sola Saraki baban Sanata Bukola ya kafa, duk wannan gogewar bai hana aka kirani ni ba ‘yar jiha ba ce jihar da na fi shekara 30 cikinta Ka gani mata na fuskantar tirjiya a siyasar Arewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *