Sarkin Musulmi ya nemi musulmi da su fara duban sabon wata Muharram

Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya umarci musulman Nijeriya su fara duban watan Muharram na shekarar 1441 daga Jumu’a 30 ga Augusta..

Ganin watan ne sabuwar shekarar musulunci za ta soma. Watan Muharram yana cikin watanni alfarma da Alqur’ani ya ambata tare da Rajab da Zulkida da Zulhajj.

Abubakar ya fitar da sanarwar ne wadda Wazirin Sokoto Farfesa Sambo Junaidu ya sanyawa hannu amatsayinsa na shugaban dubin wata a fadar Sarkin musulmi.

Sarkin musulmi ya roki Allah ya taimaki musulmi a cikin harkokin addini.

Haka kuma gwamnatin jihar Osun ta ayyana Jumu’a hutun ma’aikata saboda gudanar da shirye-shirye sabuwar shekara. Gwamnati ta yi wannan sanarwa ta hhannun Adebisi Obawale, mai kula da ma’aikatar harkokin cikin gida.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *