Spread the love

Maigirma Ministan sadarwa na Kasarmu Nigeria Dr Isah Ali Ibrahim Pantami ya umarci shugabannin gudanarwa a hukumar dake lura da kafofin sadarwa na Nigeria “Nigerian Communications Commission” (NCC) da su yi amfani da karfin ikonsu wajen yin kwakkwaran bincike game da korafin da ‘yan Nigeria suke yi kan yadda ake cire musu kudin sayan data na kamfanonin waya ba bisa ka’ida ba

Maigirma Ministan yace; dole ayi abinda ya dace wajen cika umarnin da Maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar akan haka, Ministan ya gabatar da jawabin ne a yau bayan ya saurari bayanai daga bakin babban jami’i a hukumar dake lura da harkan sadarwa Farfesa Umar Garba Danbatta

Alhamdulillah canji yazo mana da taimakon Allah, za’a fara garambawul daga kan data wanda muke saya mu hau kafar yanar gizo da dandalin sada zumunta.
Muna fata za’a zo kan kudin da ake cirewa ‘yan Nigeria a lokacin kiran waya wanda ya wuce kima da rashin tausayi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *